Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, ya umarci kamfanin samar da takin noma na jihar (JASCO) da ya fara siyar da buhunan taki sama da 1,700,000 ga manoma a fadin jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi, ne ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba sarkin Dutse Dakta Nuhu Muhammadu Sanusi a gidan gwamnatin a Dutse.
- Sakacin Gwamnati Ya Janyo Harin Gidan Yarin Kuje – PDP
- Ba Zan Barwa ‘Ya’yana Gadon Komai Ba – Buhari
Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen ganin manoma sun samu takin akan lokaci a farashi mai sauki a wannan damina.
Mataimakin gwamnan ya ce harkar noma ta samu ci gaba a sakamakon shirye-shirye da tsare-tsare daban-daban da gwamnati ta bullo da su wanda ya haifar da rage fatara da samar da ayyukan yi da samar da abinci a jihar.
Da yake karin haske kan siyar da takin, manajan-daraktan kamfanin samar da takin noma na Jigawa, Alhaji Rabiu Khalid Maigatari, ya ce za su sayar da buhu daya na NPK 20.10.10 kan Naira 15,000.
Ya ce tuni sun samu isar da manyan motoci sama da 160 wanda yayi daidai da metric ton 4,500 na kayayyakin kuma an raba su ga shaguna sama da 45 a fadin jihar.