John Robert Bolton, wanda aka san shi da katobara, ya ja wa Amurka babbar matsala ta hanyar fadin gaskiya.
Jami’in, wanda ya yi aiki a matsayin mai ba da taimako kan harkokin tsaron kasa a lokacin gwamnatin Trump, ya tabbatar yayin wata hira da kafar yada labarai ta kasar a ranar Talata cewa, ya taimaka wajen shirya juyin mulki a wasu kasashe.
Hakika dai, an dade da gano cewa Amurka ta shirya juyin mulki a wasu kasashe.
Cibiyar Cato ta bayyana cikin watan Afrilun bana cewa, Amurka ta horar da wasu sojojin da suka yi juyin mulki a akalla kasashen yammacin Afrika 4, cikin shekaru biyu da suka gabata, wadanda suka hada da Burkina Faso a 2022 da Guinea a 2021 da Mali a 2020 da 2021. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)