Mahaifin Binta Abdullahi wadda akafi sani da Binta Dadin Kowa Malam Saidu Abdullahi ya bayyana yadda ya rasa ‘yar sa Binta sanadiyar ciwon Ulcer da Thypoid da ta yi fama dashi tsawon watanni uku.
Malam Abdullahi yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a lokacin da ake ci gaba da zaman makokin jarumar ya bayyana cewar watanni uku da suka gabata Binta ta kwanta ciwon, da muka tafi asibiti sai likitoci suka tabbatar mana da cewar Ulcer da Thypoid ke damunta ba wani abu ba.
- Gwamnonin PDP Sun Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Tsadar Rayuwa
- Xi Ya Taya Stubb Murnar Zabarsa A Matsayin Shugaban Finland
Hakan yasa muka nemi shawarwarin likitoci kuma suka rubuta mana magungunan da ya kamata mu samu sai muka koma gida ta ci gaba da amfani dashi in ji Malam Abdullahi.
Ya ci gaba da cewa gab da za ta rasu ta samu sauki sosai domin har takan fito waje ta dan zauna a waje a wasu lokutan, idan tana bukatar wani abu sai ta aika a sayo mata ta yi amfani dashi.
Daga karshe dai Allah madaukakin sarki ya dauki rayuwarta da sanyin safiyar ranar Lahadi, bayan fama da doguwar jinya ta tsawon watanni biyu zuwa uku.
Da yake amsa tambayoyi a kan ko Binta kafin ta rasu ta taba yin aure, mahaifin nata ya tabbatar da cewar kafin Binta ta rasu ta taba yin aure sau daya, amma tun bayan da mijinta ya rasu a wani tsautsayi da ya faru dashi a lokacin da yake sauke farali a kasar Saudiyya bata kara yin aure ba.
Ta rasu tabar yaronta Abdul mai kimanin shekaru bakwai da haihuwa, Malam Abdullahi ya yi addu’ar Allah SWA ya yi wa Binta rahama ya kyautata makwancinta ya kuma albarkaci abin da ta bari.