• English
  • Business News
Sunday, July 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Amurka

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Amurka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

Jiya Juma’a 16 ga wata ne, memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a yayin da suke halartar taro kan harkokin tsaro a birnin Munich na kasar Jamus.
Jami’in na kasar Sin ya ce, shugaba Xi Jinping da shugaba Biden sun gana a karshen shekarar bara, inda suka yi musanyar ra’ayi kan wasu muhimman fannoni na dangantakar kasashen biyu, tare da cimma maslaha. Ya ce babban aikin dake gabansu a halin yanzu shi ne, tabbatar da “Mahangar San Francisco” a zahiri, da raya dangantakar Sin da Amurka cikin dogon lokaci kuma ta hanyar da ta dace.

Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kana, Taiwan, wani bangare ne da ba za’a iya ware shi daga babban yankin kasar Sin ba. Wannan shi ne hakikanin halin da ake ciki game da batun Taiwan.

  • ‘Yansandan Tekun Kasar Sin Sun Kori Jirgin Ruwan Kasar Philippines Da Ya Yi Kutse Cikin Yankin Ruwan Tekun Dake Kewaye Da Tsibirin Huangyan
  • Adadin Zirga-zirgar Fasinjoji A Jiragen Kasa Ya Zarce Miliyan 230 A Rabin Farko Na Wa’adin Hutun Bikin Bazara

Kaza lika, Wang ya ce yunkurin korar kasar Sin bisa hujjar kawar da hadari, gami da yunkurin mayar da kasar Sin saniyar ware, ko kuma katse mu’amala da ita da kasar Amurka ke yi, zai lahanta ita kanta Amurka. Wang ya kuma bukaci Amurka da ta soke takunkumin da ta sanyawa wasu kamfanoni, gami daidaikun mutane na kasar Sin ba bisa doka ba, don kaucewa illata hakkokin kasar Sin na samun ci gaba.

Bangarorin biyu sun kuma tattauna kan yadda za su kara mu’amala a matakai daban-daban a nan gana, da cimma matsayar ci gaba da yin mu’amala tsakanin su, da ci gaba da aiwatar da “Mahangar San Francisco”. (Murtala Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Thypoid Da Ulcer Ne Suka Yi Ajalin ‘Yata – Mahaifin Binta Dadin Kowa

Next Post

Na Kamo Hanyar Cika Burina A Harkar Fim -Zainab

Related

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali
Daga Birnin Sin

5 hours ago
Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal
Daga Birnin Sin

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

6 hours ago
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

7 hours ago
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

8 hours ago
Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

10 hours ago
Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya
Daga Birnin Sin

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

11 hours ago
Next Post
Na Kamo Hanyar Cika Burina A Harkar Fim -Zainab

Na Kamo Hanyar Cika Burina A Harkar Fim -Zainab

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

Wang Yi: Amfani Da Karfin Soji Ba Bisa Ka’ida Ba Na Ingiza Karuwar Tashin Hankali

July 5, 2025
Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal

July 5, 2025
‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027

‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027

July 5, 2025
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

July 5, 2025
Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

July 5, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

July 5, 2025
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

July 5, 2025
Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

July 5, 2025
Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

July 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci