Rundunar ‘yansandan jihar Nasarawa ta cafke wata kungiya, wadda ta kware wajen sace yara da sayar da su a fadin kasar nan.
Rundunar, ta bakin jami’in hulda da jama’a (PPRO), DSP Ramhan Nansel, ta ce ‘yan kungiyar mai mutum 10, sun sace tare da sayar da yara 45 ga mutane daban-daban kawo yanzu.
- Yawan Man Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Da Ganga 177,000 A Janairu
- Ƙungiyar Ƙwadago Za Ta Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Adawa Da Tsadar Rayuwa
DSP Nansel, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce, mambobin kungiyar sun hada da mata takwas da maza biyu.
wadanda ake zargin su ne, Hassana Jacob mai shekaru 30; Elishua Idoko, 43; Gloria Ene, mai shekaru 38; Abdulkarim Abubakar, 52; Ramatu Ibrahim, 41; Victoria Cosmos, 52; Eforma Lahadi, 41; Dorcas Ologbo, 50; Sherifat Amuda mai shekaru 45 da Ismaila Adamu.