Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ta Kafa wani kwamiti na mutane 27 wanda zai tabbatar da abin dokar bunƙasa wadatar abinci da haramta boye shi a jihar.
Hakan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren Gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Aliyu Yar’adua ya sanya hannu sannan ya rabawa manema labarai a Katsina.
- Gwamna Dikko Zai Sake Tsarin Babbar Kasuwar Jihar Katsina
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Masallata Uku Da Sace Mutane Da Dama A Katsina
Sanarwar ta ce akwai wakilan Kwamishinonin da abin ya shafa da hukumomin tsaro da sarakuna da kwamandojin Hizba da hukumar kiyaye haɗura ta KASSAROTA da wakilan kungiyoyin addini duk acikin kwamitin
Sauran sun haɗa da ma’auna da dillalan hatsi da yar tireda da Direbobi da masu motocin haya sai kuma jami’i daga ofishin gwamna wanda zai kasance sakataren kwamitin.
Ayyukan da Kwamitin zai yi sun haɗa da:
1. Gano manyan ‘yan kasuwar hatsi da ke faɗin jihar Katsina
2. Faɗakar da su akan illolin ɓoye hatsi da nufin cin ƙazamar riba da yin dukkan abinda kan iya jaza tashin farashin abinci.
3. Gayyato duk masu ruwa da tsaki akan abinda ya shafi farashin abin don bullo da hanyoyin magance matsalar hauhawar farashi.
4. Daidaita farashin hatsi ta hanyar toshe dukkan abinda kan haddasa hauhawar farashin.
5. Sanya ido akan cinikayya da jiglar kayan abincin a cikin jiha da kuma hana fita da shi ta kan iyakokin kasa da ƙasa.
6. Zakulo mutanen da suke ɓoye kayayyakin abinci.
7. Fasa dukkan wurin da aka ɓoye hatsi kana a sayar da shi akan farashin da ya dace.
8. Yin aiki tare da jami’an tsaro wajen ganowa tare da kama duk wanda aka samu ya karya doka.
Ana sa ran cewa za a ƙaddamar da Kwamitin a ranar Laraba, 21/2/2024 a Gidan Gwamnati da ke Katsina da karfe 11 na safe, idan Allah Ya kai mu.