‘Ƴan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen Gindin Dutse Makyali na Kajuru, ya yi sanadin jikkatar mutum 15 bayan an cinna wa gidajensu wuta, in ji Isa Yusuf, wani shugaban matasan yankin a hira ta wayar tarho da kamfani dillancin labarai na Anadolu.
Kafar yada labarai ta TRT Afrika Hausa ta rawaito cewa, wasu ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Kajuru da ke Kaduna a arewacin Nijeriya ranar Lahadi inda suka ƙona aƙalla mutum 12 da ransu, a cewar mazauna yankin.
- Daga Dajin Kajurun Kaduna ‘Yan Bindiga Ke Zuwa Su Addabe Mu – Mazauna Abuja
- Za Mu Ɗauki Mataki Kan Duk Masu Sukar Shugaba Tinubu Kan Tattalin Arziƙi – Bello Matawalle
Harin, wanda ƴan bindigar suka kai a ƙauyen Gindin Dutse Makyali, ya yi sanadin jikkatar mutum 15 bayan an cinna wa gidajensu wuta, in ji Isa Yusuf, wani shugaban matasan yankin a hira ta wayar tarho da kamfani dillancin labarai na Anadolu.
“Sun yi ta buɗe wuta, abin da ya sa muka ji tsoron fita daga gidajenmu. Don haka, sai suka cinna wuta a gidajen mutane inda suka kashe mutum 12 a cikin gidajensu, kana mutum kusan 15 suka ji munanan raunuka,” a cewarsa.
Isa Yusuf ya ƙara da cewa ƴan bindigar sun ƙone gidaje 17, yana mai cewa an kai mutum 15 da suka ji raunuka asibitin da ke kusa domin kula da su.
Mai magana da yawun ƴan sandan Kaduna Mansur Hassan ya tabbatar wa Anadolu aukuwar lamarin, yana mai cewa an tura ƙarin ƴan sanda na musamman yankin domin “hana kai ƙarin hare-hare da kuma kwantar da hankulan mazauna yankin.”