Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin kara kudin wutar lantarki ta hanyar janye tallafin wutar lantarki.
Majalisar dattijai ta yi wannan kiran ne ta hanyar gabatar da kudirin da ta gabatar a zamanta na ranar Laraba a Abuja.
- Tsadar Rayuwa: Ku Janye Tallafin Wutar Lantarki – IMF Ta Shawarci Gwamnatin Tarayya
- OPEC Ta Samar Da Dala Biliyan 1.7 Don Bunkasa Wutar Lantarki A Afirka
Wannan kudiri mai taken “Shirin Karin kudin wutar lantarki da kuma Biyan Kudi na Kamfanonin Rarraba wutar lantarki (DisCos) ba bisa ka’ida ba” da kuma kawo wasu al’amura masu muhimmanci ga jama’a, wanda Sen. Aminu Abbas (PDP Adamawa) da wasu 10 su dauki nauyi gabatar da shi.
Abbas ya ce akwai damuwa jin shirin kara kudin wutar lantarki daga hukumar duk da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi da irin talauci da tsadar rayuwa a Nijeriya.
Ya fadi abunda aka ruwaito Ministan Wutar Lantarki na cewa “Dole ne al’ummar kasar su fara tafiya a kan tsarin kudin, domin a halin yanzu kasar na bin bashin Naira Tiriliyan 1.3 ga kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) da dala biliyan 1.3 ga kamfanonin iskar gas.
A cewar Abass, Ministan ya ce ana bukatar sama da Naira Tiriliyan 2 don tallafin, amma Naira biliyan 450 ne kawai aka yi kasafin shekarar 2024.