Asirin wata yarinya mai shekara 22, wadda ta shafe shekara biyu cir, tana satar yara, ta kai wa mahaifinta wanda shi kuma ke kai wa masu garkuwa a jihar Ondo, ya tonu.
Wadda aka kaman mai suna Adeola Omoniyi, ta shafe shekara biyu cir tana kama kananan yara tana ba mahaifinta, mai suna Ilesanmi Omoniyi, yana yin garkuwa da su, a kan ladan naira 30,000 ga kowane daya.
Wadda ake zargi da laifin na hada-kai wajen yin garkuwar, an garkame ta, tare da mahaifin nata a hedikwatar ‘yansanda da ke karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.
Da take bayani kan yadda suka hada-kai da mahaifin nata,suke aikata wannan laifin cewa ta yi “Ni ina daga cikin masu garkuwa. Ina daukar kananan yara ne in yi garkuwa da su, idan na dauke su, sai in kai su gidanmu wajrn babana a Igbotako. Na samu sa’ar sace yara biyu, kafin in kai su maboya, sai aka kama ni”.
“Idan na kawo wa mahaifina wanda na sato, yana ba ni naira dubu talatin, a kan kowane yaro. Da irin wadannan kudin da nake samu ne nake daukar dawainiyar kaina. Ni ban san, ya yake yi da wadannan yara ba. Ni dai kawai in na sato sai in kawo masa”. “Shi ke sa ni, in sato masa yaran. Na sato yaron farko daga Ilutitun.
“Lokacin da na sato yaron, mahaifiyar yaron ta kwalla ihu.
Nan da nan mutane suka taso min, suka kama ni suka kai ni wajen ‘yansanda, daga nan aka wuce da ni Akure.
“Na fara satar kananan yara tare da yin garkuwa da su, tun shekara biyu da suka wuce. “Na sace yaro na farko ne a shekara ta 2021, sa i yaro na biyu a bana.” Sai dai mahaifin yarinyar da ake zargin ya ce, tuni suka yi barankan-barankan da ita.
Na san dai tana zaune a Legas. Ta kai shekara biyu a can, tun da ta tafi, sai lokacin da ta kamu da rashin lafiya aka zo da ita Igbotako.
Na dauke ta na kai ta coci, amma sai faston ya ce, sai na ba shi naira 80,000. Ai daga baya ya gaya min cewa, ta samu sauki, amma bayan ‘yan kwanaki kadan, bayan karbar wannan kudi, sai ta gudu ta bar cocin.
“Ni ce wadda nake sato kananan yara in kawo masa, in ji yarinyar. Shi kuwa uba cewa ya yi bai ba ta naira 30,000 ba. Tun kimanin wata shida bayan ta bar cocin, muke ta nemanta, sai na ji, tana satar yara.”
Bugu da kari, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan na jihar, SP Funmi Odunlami, ya tabbatar da cewa, da zarar sun gama bincikensu za su gurfanar da wadda ake zargin gaban kuliya.