Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta ce ta yi rajistar mutane 411 da aka tabbatar sun kamu da cutar sannan 72 sun mutu sakamakon zazzabin Lassa a fadin jihohi 21 na tarayyar kasar daga mako daya zuwa mako shida na shekarar 2024.
Hukumar NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na yanar gizo ranar Alhamis.
- Zazzabin Lassa Ya Yi Ajalin Mutum 154 A Nijeriya —NCDC
- Diphtheria: Mutane 123 Sun Kamu, 38 Sun Mutu A Jihohi 4 – NCDC
Hukumar ta bayyana cewa adadin sabbin wadanda aka tabbatar sun karu daga 70 a cikin mako biyar zuwa 83 a cikin mako shida, tare da samun mutuwar mutane tara a cikin mako shida, wanda ya kai 5 ga Fabrairu zuwa Fed. 11.
A cewar NCDC, kashi 65 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun fito ne daga jihohin Ondo da Edo da Bauchi, yayin da kashi 35 cikin 100 aka samu rahoto daga jihohi 17.
Hukumar ta ce adadin wadanda ake zargin sun kamu a shekarar 2024 (2,122) ya ragu idan aka kwatanta da adadin da aka bayar a daidai wannan lokacin a shekarar 2023 (8,280).
Ya ce mafi yawan shekarun da zazzabin Lassa ya shafa sun kai shekaru 21 zuwa 30, kuma sababbin ma’aikatan lafiya biyu sun kamu da cutar a cikin makon da ya gabata.
Hukumar NCDC ta ce, an fito d tsarin kula da masu fama da cutar zazzabin Lassa na kasa, da tsarin kula da al’amuran da suka shafi bangarori daban-daban don daidaita a dukkan matakai a Cibiyar Ayyukan Gaggawa (EOC).
Hukumar ta kuma zayyana wasu daga cikin kalubalen da take fuskanta a yakin da take da zazzabin Lassa a fadin kasar nan, wadanda suka hada da gabatar da cutar a makare da kuma rashin kyawun yanayin neman lafiya sakamakon tsadar magani da kula da lafiya.
Sauran ƙalubalen, in ji shi, sun haɗa da rashin tsabtar muhalli da kuma rashin fahimtar da ake gani a cikin al’ummomi masu dauke da ita.