Yanzu dai an gano fiye da mutane 1,000 ne Hukumar Lafiyar ta Duniya ta samu labarin sun kamu da cutar daga kasashe 29 wadanda basu daga cikin wadanda ba kasafai bane, ake samun kwayar cutar a cikinsu.
Babbanjami’i kuma Shugaban hukumar Tedros Ghebreyesus, shi ne wanda ya bayyana hakan lokacin da ya gabatar da wani jawabin da aka yada ta kafar sadarwar zamani ta hukumar.
Mista Ghebreyesus ya kara jaddada bayanin cewar yadda wasu kasashe suka bada rahoto kan cutar mai yaduwa, abin ya nuna ba kawai sai maza masu neman maza bane,suke kamuwa da cutar Kyandar Biri ba.Domin kuwa yanzu an samu har ma wasu kasashe ana samun wadanda suka kamu da cutar tsakanin mace da mace.
Ya ce cutar Kyandar Biri ta dade tana samar da babbar matsala da bazuwa a nahiyar Afirka inda ta kashe al’ummar ta,shekaru masu yawa da suka gabata saboda zuwa yanzu an samu wadanda suka kamu da cutar sun kai 1,400 da kuma mutuwar mutane 66.
Ya cigaba da bayanin cewa“ Wannan ba abinda yakamata da duniyar da muke ciki,yadda su kasashen da suke kallon kansu sun waye yanzu suna maida hankali ne kan cutar ba domin komai ba sai don ta bayyana a kasashe masu samun kudaden shiga masu yawa.
“Wuraren da suke tare da barazanar kwayoyin cutar sune yakamata a basu kulawa ta musamman, bugu da kari duk wadansu abubuwan da suka kamata a taimaka masu kamar dai yadda aka ba wadanda suka dara su cigaba domin su kare kansu.,” Ya kara jaddada bukatar samar da kulawar lafiyar a kasashen da ke nahiyar da suke tare da kwayoyin cutar.
Kamar yadda alkalumma suke a kafar sadarwar zamani ta hukumar lafiya ta duniya a kasashen da basu da wata damuwa dangane da cutar,ya zuwa 22 ga watan Mayu 2022 kasar Ingila ita ce jagaba da yawan mutanen da suka kamu da cutar da suka kai fiye da 100 daganan kuma sai kasashen Portugal da Canada
Idan kuma aka duba ta bangaren nahiyar Afirka jamhuriyyar kasar damukuradiyya ta Congo ita ta kasance jagora da mutanen da suka kamu da cutar1,284,sai wadanda suka rigamu gidan gaskiya 58 tsakanin1 ga watannin Janairu zuwa 8 ga Mayu 2022,yayin da kasashen Nijeriya da Kamaru suka bin sahunta.