A Nijeriya baya ga noman damina da manoman kasar ke yi, akwai kuma manoman da ke yin noman rani bayan daminar ta wuce, inda hakan ke kara taimaka musu wajen kara samar wa da kansu kudi da kuma kara wadata kasar da abinci.
Wasu masana na ganin cewa kokarin nasu bai kai ga yadda za a iya yayata wa ba, domin kuwa a ganinsu da a ce ana aiwatar da abubuwan da ake fada a baki, da yanzu kasar ta dara takwarorinta da suka yi mata nisa wajen noman rani.
A cewar masanan, Nijeriya za ta iya shiga gaban kasar Masar, wajen noman tumatir, saboda idan ka duba, kashi saba’in cikin dari na kasar Masar sahara ce, inda kuma Nijeriya, Allah ya albarkace ta da kasar noma mai inganci, amma ba ma bin hanyoyin da suka dace.
Masana dai na da ra’ayin cewa, hukumomi a Nijeriya har yanzu ba sa fargabar ganin yadda suke yi wa sashin na noma rikon Sakanaira Kashi.
Duk da cewa kasar na daga manyan masu noman tumatur a duniya, har yanzu kasar na shigo da tumatur daga kasashen waje.
Alhaji Abdulrahim Ali, wani manomi a karamar hukumar Kura ta jihar Kano, ya sanar da cewa, suna noman tumatir, amma idan masu siya ba su zoba ba, dole ne mu dauka mu kai kasuwa mu siyar da araha.
Shi kuwa Malam Danlami Umar, sakatare na Kungiyar masu sai da kayan gwari ta jihar Kano, ya bayyana cewa, wannan shi ne lokacin da ake asara, saboda tsananin tsadar da kayan ke da shi.
Ya kara da cewa, idan ka je gonar wani manomin za ka samu kaya mai yawa.
Kokarin Gwamnati
Kwamishinan noma na jihar Kano Alhaji Musa Sulaiman Shanono ya ce, gwamnatin tana kokarinta wajen magance wanan matsala.
Alhaji Musa ya kara da cewa, gwamnati tana sane kuma ta damu kwarai, saboda haka gwamnatin kano ta kulla yarjejeniya domin samar da kamfanin da zai dinga sarrafa tumatir domin taimaka wa manoma.