A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mutum 37 don duba lamarin samar da mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan, an ba kwamitin umarnin tabbatar da fitar da tsarin mafi karancin albashi tare da la’akari mastalolin da al’ummar Nijeriya kie fuskanta a bangaren tattalin arziki da sauransu.
A ra’ayinmu, wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci, an kuma umarci ‘yan kwamitin su fito da mafi karancin albashin da zai samu karbuwa ga dukkan matakan gwamnati. An kuma nemi su yi nazari tare da fitar da dalilan da ya hana wasu jihohi aiwatar da mafi karancin albashin da aka aiwatar a baya.
- BUA Ya Sanar Da Ƙarawa Ma’aikatansa Albashi Kashi 50 Cikin 100 Saboda Tsadar Rayuwa
- NLC Na Neman A Biya Ma’aikata Naira Miliyan Ɗaya A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashi
In aka lura da wanann umarnin daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu za a fahimci cewa, shugaban kasa ya damu da al’amarin matsin rayuwu da ya shafi ma’aikatan gwamnati ne kawai. Amma in aka lura za a iya fahintar cewa, wannan ba karamin kuskure ba ne, don ya kamata a ce an samar da wata mafita ga ma’aikata masu aiki a bangaren kamfanoni masu zaman kansu domin suma suna fuskantar matsin rayuwa da dukkan ‘yan Nijeriya ke fuskatanta.
Amma kuma a ra’ayinmu, ya kamata a fahinci cewa, ‘yan Nijetriya da suke aiki a kamfanoni masu zaman kansu suma suna fuskantar matsalolin tattalin arziki da tsadar rayuwar da ake ji a halin yanzu. Haka kuma wadanda ma basa wani aiki na gwamnati ko kuma ma masu zaman kansu suma suna fatan gwamnati ta sa su a lissafi ta yadda za su samu jin saukin tashin farashin kayayyaki da zai faru in an kara wa ma’aikata albashi.
Zuwa yanzu, bangarorin da ya ke tattaunawa a kan mafi karancin albashin sun fara ayyana wasu manyan kudade da ba zai a iya aiwatarwa ba. A ra’ayinmu, maimakon a ayyana wani albashi masu yawa wanda ba za a iya aiwatarwa ba, daga kaarshe abin ya tsaya kawai a takardar ba tare da an iya aiwatarwa ba. ya kamata a samar da tsarin da zai samu karbuwa ga dukkan bangarori. Ya kuma kamata a cire dukkan abin da ya shafi siyasa da son rai wajen aiwatar da mafi karancin albashin, musamman ganin irin wahalar da al’umma ke fama da shi a wannan lokacin.
A sharhin da muka gabatar a baya mun nemi a kara wa ma’aikata albashi, albashin da zai dauki dawainiyar rayuwar ma’aikaci. Za kuma mu ci gaba da da’awar neman a a tabbatar da an kara wa ma’aikacin Nijeriya albashi. A bayyana yake cewa, duk irin kudin da aka biya mai karbar albashi ba zai taba isansa tafiyar da raywuarsa ba.
A cikin sharhin da muka yi mun nemi gwamnati ta sa hannu a dukkan bangarorin rayuwar al’umma Nijeriya gaba daya ba wai na masu karbar albashi kawai ba, al’amarin ba kawai na albashi ba ne, harma na abin da albashin zai iya saya.
Wannan ne ya kawo mu a kan bukatar a gagguta sake fasalin albashi da tattalin arzikin kasa baki daya. Ta yadda za a samu saukin farashin kayan masarufi. Duk da cewa, babu yadda albashi zai iya biya wa ma’aikaci bukatarsa amma albashin ya zamana zai iya raka ma’aikaci zuwa wani mataki mai muhimmanci a duk wata.
A ra’ayinmu duk yawan albashin da za a ba ma’aikaci a karshen wata ba zai taba isarsa ba in har aka ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi.
Yana da muhimmanci mu jawo hankalin gwamnati a kan tsadar kudin sufuri wanda a halin yanzu gwamnati ta bari a hannun bangarori masu zaman kansu, wanda suke amfani na lallacewar hanyoyinmu da hauhawar farashin albarkatun man fetur wajen tsawwala farashin kudin mota. A yayin da babu tsarin sufuri na gwamnati, kudaden sufurin da ma’aikaci zai ci gaba da kashewa zai ci gaba da hauhawa a waasu lokutta ma ba zai iya biya ba saboda tsada, duk kuwa da yawan albashin da gwamnati za ta ba ma’aikaci.
A bangaren kiwon lafiya, ‘yan Nijeriya da ke aiki a bangaren gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu ba su da wani tsarin kula da lafiya da zai tabbatar da kula da lafiyarsu dana iyalansu. Asibitocin gamnati da ake da su suma suna gwa-gwa ne da asibitoci masu zaman kansu wajen tsada.
Haka kuma, a kullum sai ka ji gwamnati na bayanin wai muna da gibin gidaje fiye da miliyan 16 amma kuma har yanzu bamu ga abin da ta yi ba don magance lamarin. A bangaren ilimi kuma, kusan gwamnati ta saki makarantu a dukkan mataki ga hannun masu zaman kansu.
A bayyana yake cewa, harkokin kasuwanci na tafiya a kasar nan ne tamkar babu gwamnati, ‘yan kasuwa sun zama gwamnatin kansu ta hanyar samar wa kansu abubuwan tafiyar da harkokinsu kamar, hanyoyi, ruwa, wutar lantarki da sauransu. Gwamnati na tuna dasu ne kawai in lokacin karbar haraji ya yi amma ba wai a yi muusu ayyyukan da zai sa su ji dadin tafiyar da harkokin kasuwancinsu ba.
Wadanan ko-in-kular ke kara zama kalubale ga tattalin arziki, musamman shi ne ke karya darajar kudin da ake karba da sunan albashi. Dole a ba gwamnati shawarar mayar da hankali a kan daukar matakan tabbatar da tattalin arzkin kasa yana tafiya.
A ra’ayinmu, in har ana bukatar a samu ma’aikatan gwamnati da za su bayar da gudumawarsu wajen gina kasa dole a samar da tsarin tattalin arzikin tare da yaki da hauhawar farashi in ba haka duk karin albashin da za a yi zai zama matakin karin wahala ne kawai ga ma’aikata da sauran al’ummar Nijeriya.