Shugaban majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, muhimman bangarori da kwamitin gyaran kundin tsarin mulki ke yin kwaskwarima zai gyara kura-kuren da aka samu a lokacin zaben 2023.
Abbas ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi wajen kaddamar da kwamitin gyaran kundin tsarin mulki a Abuja. Ya ce akwai bukatar gyara wasu muhimman bangarori na tsarin mulki wanda majalisa ta dukufa wajen ganin an gyrasu domin karfafa harkokin shugabanci.
- Akwai Hannun Gwamnan Kano Wajen Fitar Da Murja Kunya Daga Gidan Gyaran Hali – Jaafar Jaafar
- A Bara Adadin Dalibai Sinawa Dake Karatu A Manyan Makarantu Ya Kai Sama Da Miliyan 47
A cewarsa, wadannan bangarori suna da mutukar muhimmanci ga dimokuradiyyar Nijeriya da kuma tabbatar da abubuwan da tsarin shugabanci ke bukata ga ‘yan Nijeriya.
Ya ce an gabatar da kudurori daban-daban kan lamarin a tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai da ke da mutukar muhimmanci.
Shugaban majalisar ya bukaci kwamitin ya yi aiki kan kudurin majalisa ta 10 domin farfado da harkoki shugabanci a kasar nan.
Ya ce tuni dai majalisar take aiki kan tsarin gyaran kundin mulki da kuma lokacin da majalisar kasa ta amince da shi na kammala gyaran.
A bangare daya kuma, mataimakin shugaban majalisar wakilai kuma shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulkiin, Hon. Benjamin Kalu ya ce za a samar da sabon tsarin kundin mulki kafin 2025.
Kalu ya ce za a bai wa dukkan ‘yan Nijeriya damar bayar da tasu gudummuwa wajen kokarin sake fasalin makoman Nijeriya a cikin gyaran kundin tsarin mulkin.