Lokacin Da Ya Fi Dacewa Da Noman Tumatir
Nijeriya na daya daga cikin kasasen da ke kan gaba wajen noman tumatir, musamman ganin cewa gidaje da dama na amafani da shi.
An fi yin noman tumatir a lokacin kakar rani, inda hakan ya sa ake yawan karancin sa a lokacin kakar damuna, domin kuwa nomansa a lokacin damuna, na da matukar wahala sakamakon yawan lema da ake samu a lokacin.
Ana yin girbin tumatar ne bayan kwana 60 zuwa 90, ya danganta da nau’in wanda aka shuka, ana kuma renon shuka Irinsa daga sati uku zuwa hudu.
Abin Da Ya Kamata A Sani Game Da Noman Tumatir:
Takin Gargajiya: Ana so a sanya takin gargajiya a cikin jerin kayan da za a yi amfani da su wajen noman tumatir, haka nan ana so a tabbatar da kasar noman da za a shuka tumatirin na da kyau.
Maganin Feshi: Ya kamata manomi ya tabbatar ya tanadi maganin feshi, don kare tumatirinsa daga harbin kwari ko cututtukan da ke yi masa illa.
Matakan Cin Nasara Wajen Noman Tumatir:
Samar Da Gonar Da Ta Dace:
Samar da gonar da za a noma shi na da matukar kyau, sannan kuma a tabbatar akwai hanya zuwa shiga gonar da fitar da shi a cikin suki zuwa kasuwa.
Daukar Ma’aikata: Ana bukatar a dauki mutane aiki; wadanda za su rika lura da shi, musamman wajen nome shi tare da yi masa feshi.
Ban Ruwa: Yana da kyau a tabbatar da an mallaki kamar rijiyar burtsatsai ko ta bohol a gonar da aka shuka shi, domin yin ban ruwa.
Zabo Ingantaccen Iri: Ana bukatar manomi ya tabbatar ya samo ingantaccen Irin da zai shuka, musamman don samun riba mai yawa.
Ingantaccen Maganin Feshi: Ana so a samu maganin feshin da ya dace da tumatirin da aka shuka, don saurin kashe cutar da ta harbe shi, domin tumatir na fuskantar nau’ikan cututtuka iri daban-daban a lokacin da aka shuka shi.
Sannan kuma, wajibi ne manoninsa ya tabbatar ya kiyaye wajen yin feshin yadda ya dace.
Har ila yau, ana so namomi ya tabbatar da ya kare ganyen tumatar daga taba kasa, don gudun ka da ya lalace.
Lokacin Girbi: Da zarar ya nuna; ana so a gagguata cire shi don gudun ka da ya lalace ko ya rube, sannan bayan girbin an fi so a ajiye yi shi a sarari.
Kasuwancinsa: Kafin shuka tumatir, ana so ka tabbatar ka fara tuntubar masu saye tare da yin bincike kan yadda hada-hadarsa ke tafiya a kasuwanni.
Shin Kana Son Sayar Da Shi A Kasuwa Ko A Manyan Shaguna?
Ya kamata manomi ya yi tunanin a ina ne zai sayar da shi bayan ya girbe shi, domin wasu manoman na kai shi kasuwa ko wasu manyan shaguna; don sayarwa.
Wasu manoman kuma, suna kai shi ne kai tsaye zuwa manyan gidajen sayar da abinci ko otel-otel don sayarwa.