• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyautatawa Al’umma Ita Ce Kashin Bayan Ci Gaban Ko Wacce Kasa

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Kyautatawa Al’umma Ita Ce Kashin Bayan Ci Gaban Ko Wacce Kasa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yau Talata ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar Kasar Sin, inda firaministan kasar, Li Qiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati a bara. Cikin rahoton ya bayyana cewa, “Gwamnati ta cimma nasarar samun ci gaba mai inganci, da tabbatar da zaman lafiyar al’umma, lamarin da ya sa aka sami gagarumin ci gaba a fannin gina zamantakewar al’umma ta zamani bisa tsarin gurguzu a dukkanin fannoni.”

Dukkan ci gaban kasar Sin baya rasa nasaba da irin tsarin shugabancin da ta zabarwa kanta. Tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, shi ne tushe kuma sirrin ci gaban kasar. Sin ta yi abun da ba kasafai a kan gani ba, wato ta duba yanayinta, ta kuma fadawa kan ta gaskiya, inda ta rika aiwatar da manufofi da dabarun da suka dace da yanayinta, maimakon zama ’yar a bi Yarima a sha kida.

  • Xi Jinping Ya Halarci Taron Tattaunawa A Yayin Taron Majalisar Wakilan Jama’ar Kasar Sin

Na saba da jin ana cewa, “in dambu ya yi yawa baya jin mai” wato idan mutane suka yi yawa, to da wuya kowa ya ci gajiyar wata manufa ko shirin kyautatawa al’umma. Sai dai, zan iya cewa, duk da dimbin jama’a da kasar Sin take da shi, ba na jin ana irin wannan furuci, har kullum manufofin kasar kan isa ga wadanda aka yi domin su.

Wani batu shi ne, Kishin Kasa. Ana yawaita samun rikicin addini ko kabilanci a cikin gidan kasashen duniya da dama, amma duk da yawan kabilu da addinai dake a kasar Sin, ba ka jin tashin irin wadannan rigingimu. Abun da na lura da shi da al’ummar kasar shi ne, duk da cewa akwai kabilu daban daban, tuna cewa kai Basine ne, shi ne abu na farko kuma mafi muhimmanci kafin komai. Wato an dasawa Sinawa kishin kasa da kaunar kasa kafin komai, wanda ya zama tushen zaman lafiya da zaman jituwa da hakuri da juna da ake samu tsakanin al’ummun kasar daga mabambantan kabilu.

Jawabin nasa ya kuma tabo ci gaban da aka samu a bangarorin tattalin arziki da fasahohi da kirkire kirkire, amma na mayar da hankali ne kan yanayin zaman takewar jama’a da irin ci gaban da suke samu, saboda yadda hakan ke ja hankalina matuka, kuma saboda ina kwadayin ganin an samu irin hakan a kasata da sauran sassan duniya. Duk wani yunkuri ko manufa da kasa za ta aiwatar, ba za su taba yin tasiri ba idan babu jama’a. Haka ma, duk burin samun ci gaban da take da shi, ba za ta iya cimmawa ba, muddun al’ummarta na cikin  kuncin rayuwa ko rikici da juna.

Labarai Masu Nasaba

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

A matsayin wadda ta shaida yanayin rayuwar Sinawa, tabbas zan iya cewa ci gaban kasar ya samo asali ne daga yadda ta mayar da hankali kan raya jama’arta da kyautata rayuwarsu da tabbatar da daidaito da girmama juna tsakanin mabanbantan kabilu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Ci GabafasahohiKasakirkire-kirkireKishin KasaTattalin Arziki
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ana Kokarin Rantsar Da ‘Yan APC 16 A Majalisar Filato Ta Barauniyar Hanya – Gwamnatin Jihar

Next Post

Alkaluman Sun Shaida Cewa Dole A Fahimci Ci Gaba Yayin Da Ake Kokarin Samar Da Shi

Related

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
Daga Birnin Sin

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

12 hours ago
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

13 hours ago
An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu
Daga Birnin Sin

An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

14 hours ago
Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko

15 hours ago
Sin Ta Yi Kira Da A Ci Gaba Da Himmatuwa Wajen Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Da A Ci Gaba Da Himmatuwa Wajen Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

16 hours ago
Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa

1 day ago
Next Post
Alkaluman Sun Shaida Cewa Dole A Fahimci Ci Gaba Yayin Da Ake Kokarin Samar Da Shi

Alkaluman Sun Shaida Cewa Dole A Fahimci Ci Gaba Yayin Da Ake Kokarin Samar Da Shi

LABARAI MASU NASABA

aure

Ko Kin San… Matsalolin Mahaifa Da Suke Hana Haihuwa 

July 27, 2025
VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

VON Zai Fara Watsa Shirye-Shirye Da Harshen Sinanci — Ndace

July 27, 2025
Yadda Ake Faten Acca

Yadda Ake Faten Acca

July 27, 2025
Hanyoyin Gyaran Gashi

Hanyoyin Gyaran Gashi

July 27, 2025
Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

July 26, 2025
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

July 26, 2025
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

July 26, 2025
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

July 26, 2025
al'umma

Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.