Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Talata ya jaddada muhimmancin samar da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko a bisa yanayin gida, a yayin taron shekara shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, wato majalisar dokokin kasar.
Shugaba Xi ya yi furucin ne a lokacin da ya halarci taron tattaunawa tare da ‘yan majalisar da suka zo daga lardin Jiangsu na kasar. (Yahaya)
Talla