Rawar da kasar Sin ke takawa a duniya a fagen ci gaban tattalin arziki ba a boye take ba bisa yadda masana daga sassa daban-daban suke bayar da shaida a kai.
Kamar yadda kasar ta tsara samun bunkasar tattalin arziki da kashi 5% kuma aka ga nasarar haka a sarari a shekarar 2023, a bana ma gwamnatin kasar Sin ta kuduri aniyar cimma kason a shekarar 2024.
Masana tattalin arziki da manyan ‘yan kasuwa sun yi amannar cewa gwamnatin ta Sin ta tsara cimma wannan kaso ne daidai da al’amuran dake gudana a bangaren ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma hangen nesan gwamnatin wajen tafiyar da kasa.
Firaministan kasar Sin, Li Qiang wanda ya sanar da muradin da kasar take son cimmawa a farkon makon, a yayin da ya gabatar da rahoton aikin gwamnati a gun taron bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar, inda ya nuna cewa, tabbas kasar za ta cimma muradinta yadda take so saboda damammakin da take da su na ci gaban tattalin arziki tun daga kan masana’antu da kasuwanni da ma’aikata da kuma kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha.
A wani bangare na tsare-tsarenta, kasar Sin ta kara kasafin kudinta na shekara-shekara a bangaren kimiyya da fasaha da kashi 10% zuwa Yuan biliyan 370.8 da ba a taba ganin irinsa ba, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 51.6, wanda ya kasance mafi girma tun daga shekarar 2019.
“Za mu yi kokari cikin hanzari don habaka dogaro da kai da kara karfi a fannin kimiyya da fasaha,” in ji Li, “Za mu yi cikakken amfani da tagomashin da ke cikin sabon tsarin don samar da albarkatun kasa a duk fadin kasar don daukaka matsayin Sin a sashen kirkire-kirkire daban-daban.”
Abubuwan da Firaminista Li ya bayyana, sun samu hujjoji da kawar da shakku daga bayanan wani masanin tattalin arziki da ci gaba a Jami’ar Columbia, Farfesa Jeffrey Sachs yayin da ya ce, “kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da Sin ke zurfafa kokari a kai suna samun bunkasa cikin hanzari kuma wannan ne zai dora kasar Sin a wani gawurtaccen matsayi a duniya nan da ‘yan shekaru masu zuwa.”
Har ila yau, don jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje, rahoton aikin gwamnati na wannan shekara ya gabatar da wasu matakai na musamman kamar ci gaba da rage tarnakin da kasashen waje suka fuskanta wajen zuba jari a kasar Sin.
Mataimakin shugaban kamfanin kere-kere na Panasonic dake Japan, Tetsuro Homma da shugaban sashen kayayyaki na kamfanin L’Oreal, Alexis Perakis-Valat, duk sun yi amannar cewa, fagen kasuwanci na kasar Sin na da matukar ban sha’awa tare da bayyana muradin fadada kasuwancinsu a kasar.
Bunkasar tattalin arzikin Sin ba ita kadai zai amfanar ba, har da sauran kasashen duniya, kasancewarta kashin bayan gudanar da hada-hada a duniya. Ko a shekarar 2023, ta ba da gudunmawa ga habakar tattalin arzikin duniya da kashi 32%, kamar yadda Majalisar Harkokin Kudi ta Kasa da Kasa ta bayyana.
Bugu da kari, wani bincike na Asusun Ba Da Lamuni na Duniya (IMF) ya nunar da cewa, ci gaban tattalin arzikin Sin ba ita kadai yake amfanarwa ba har da sauran duniya. Idan ta samu ci gaba da kashi daya, a kalla na sauran kasashe ya kan habaka da kashi 0.3.
Irin wannan kokari na Sin duk mutane na-gari ke fatan gani a duniya, ba kamar Amurka mai habaka cinikin makamai da danniya ga marasa karfi ba kamar yadda muke gani a Gaza da kasashen Afirka dake fama da karairayewar darajar kudi. Ko a bana, Amurka ta ba da izinin a ware wa bangaren tsaronta dala biliyan 886, an samu karin kusan kashi 3% daga na bara.