Sahur shi ne abincin da ake ci ko a sha a ƙarahen dare kafin ketowar alfijir da niyyar azumi.
Yin sahur abu ne mai tarin falala, domin lokacin yinsa, shi ne lokaci mafi tsada a cikin dare, a lokacin ne Allah yake saukowa saman duniya saukar da ta dace da shi (S.W.T). Lokacin sahur lokaci ne na karɓar addu’a da neman gafara da sauran zikirori.
1.0 Sahur yana da albarka: An karɓo daga Anas ɗan Malik, Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ” Ku yi sahur, domin lalle a cikin sahur akwai albarka” Bukhari (#1923) da Muslim (#1095).
An karɓo hadisi daga Salmanul Farisi, Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ” Akwai albarka a cikin abu uku… da yin sahur” Ɗabarani (Mu’ujamul Kabir 6/251) Salsalar hadisin mai kyau ce bisa shaidar wasu hadisai.
An karɓo hadisi daga Abdullahi ɗan Harisa daga wani daga cikin sahabban Annabi (S.A.W) ya ce: Na shiga wajen Annabi (S.A.W) a lokacin da yake yin sahur, sai ya ce:” Lalle shi (sahur) wata irin albarka ce Allah ya baku shi, don haka; ka da ku bar yinsa” Nasã’i (Almujtabã 4/148 da Sunanul Kubrã 2/79) da Ahmad (Musnad #23113, da 23142) da salsala ingantacciya.
1.1 Abinci sahur yana da albarka; yin sahur albarka ne, haka ma abincin sahur abinci ne mai albarka.
Ana karɓo hadisi daga Miƙdãm ɗan Ma’adikarib Allah ya ƙara yarda a gare shi, daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Ina horonku da cin abincin sahur, domin abinci ne mai albarka” Nasã’i (Almujtabã 4/149 da Sunanul Kubrã 2/115) da Ahmad (Musnad #17192) da salsala ingantacciya.
An karɓo daga Abud Dardã’i Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Shi sahur abinci ne mai albarka.”Ibnu Hibban (Al’ihsãn #3464) Ɗabarãni (Mu’ujamul Kabir 17/131 hadisi mai lamba 322).
An karɓo daga Irbãdu ɗan Sãriyatu Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya gayyace ni cin abincin sahur a cikin Ramalana sai ya ce: ” Tawo ka ci abinci mai albarka” Abu Dãwud (#2344) da Nasã’i (Almujtabã 4/148) da Ibnu Hibbãn (Al’ihsãn #3465) salsalar hadisin ingantacciya ce. A lafazin Nasã’i ya zo da ce: Na ji Manzon Allah (S.A.W) Yana gayyatar mutane cin abincin sahur a cikin Ramalana…
1.3 Allah yana yabon masu yin sahur, Mala’iku kuma suna yi musu addu’a.
An barɓo hadisi daga Abdullahi ɗan Umar, Allah ya ƙara yarda a gare su, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Lalle Allah yana yabon Mala’iku kuma suna addu’a ga waɗanda suke yin sahur” Ibnu Hibbãn (Al’ihsãn #3467) da Ɗabarani (Mu’ujamul Ausaɗ 6/287) da salsala ingantacciya.