Al’ummar Falasdinu sun fara gudanar da azumin watan Ramadan cikin halin kunci, daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta, inda yunwa ke kara ta’azzara a yankin Zirin Gaza yayin da har yanzu aka kasa kawo karshen yakin da Isra’ila ta kwashe watanni biyar tana yi a kan fararen hula.
“Wannan wata na Ramadan ya sha bamban da dukkan Ramadan da suka gabata,” in ji Bilal abed Rabbo mazaunin Ramallah.
A taron majalisar ministocin kasar na mako-mako, Firaministan Falasdinu Mohammed Shtayyeh, ya bayyana cewa, “Watan Ramadan ya zo a wannan shekara, yayin da al’ummarmu a Zirin Gaza ke fama da yunwa da kisa sakamakon laifukan kisan kiyashi da ake ci gaba da yi ba tare da kakkautawa ba, muna sa ran shiga tsakani.”
Ya ce suna jiran kotun duniya ta dakatar da wadannan munanan laifuka, sannan suna rokon Allah ya sanya ranakun watan nan mai alfarma ya kasance sassauci ga wadanda suke cikin ukuba, kuma a daina zubar da jini, yana mai kara cewa, Allah ne kadai yake da ikon ceto wadanda suke cikin yunwa da kuma rashin lafiya.
Falasdinawa dai na ganin cewa za a samu tashin hankali daga Yahudawan da ke kyamar Musulunci a cikin watan Ramadan.
“Na yi imanin cewa ayyukan shahada za su karu kuma tsayin daka zai karu, musamman ta fuskar al’amarin Aqsa da hana masu ibada shiga masallacin domin yin addu’a, musamman matasa,” in ji Jamal mazaunin Ramallah.
Kasashen Qatar, Masar da Amurka sun yi fatan kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta a daidai lokacin da ake gudanar da azumin Ramadan, wanda zai hada da sakin dimbin Yahudawan da aka yi garkuwa da su da kuma fursunonin Falasdinu, hadi da bude hanyoyin shigar da kayayyakin jin-kai, amma tattaunawar ta ci tura a makon jiya.
Hamas dai na neman a ba da tabbacin cewa wannan yarjejeniya za ta kai ga kawo karshen yakin, yayin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da kai hare-hare har zuwa lokacin da zai kawar da Hamas din da kuma kwato sauran Yahudawan da ke hannun kungiyar.
Yakin ya kori kusan kashi 80 na al’ummar Gaza mai mutane miliyan 2.3 daga gidajensu tare da jefa dubbai cikin matsananciyar yunwa.
Jami’an lafiya sun ce akalla mutane 20 galibi yara kanana ne suka mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin ruwa a Arewacin Gaza.
Sojojin Isra’ila sun rufe arewacin kasar tun daga watan Oktoban 2023, kuma kungiyoyin agaji sun ce takunkumin da Isra’ila ke ci gaba da kakabawa yankin da tabarbarewar doka da oda, sun sun hana isar da isasshen abinci zuwa Gaza.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa akalla Falasdinawa 31,112 aka kashe tun bayan fara yakin, ciki har da gawarwaki 67 da aka kai asibitoci cikin sa’o’i 48 da suka gabata.