Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ƙasa ta bayyana cewa Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki, Kaduna ba na zuriyar Marigayi Shaikh Abubakar Gumi ko na wani mutum ba ne, na al’ummar Musulmi ne gaba ɗaya, wanda ke ƙarƙashin kulawarta.
Ta kuma ce, naɗin mataimakin mai gabatar da Tafsiri a masallacin da aka yi, an yi shi ne bisa ƙa’ida, ba wai an yi ne don a muzguna wa wasu ko wani mutum ba.
- Sheikh Gumi Ga Tinubu: Ka Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga, Kada Ka Zama Irin Buhari
- Hukuncin Zaben Adamawa: Na Rungumi Kaddara – Binani
JNI ta ce, Limamai, mataimakansu, masu wa’azi da mataimakansu, da duk masu kula da harkar masallacin, duk suna ƙarƙashin kulawarta ne, na abin da ya shafi albashi da sauran hidindimun masallacin.
Sakataren gudanarwa na ƙungiyar JNI, Malam Yusuf Bida ne ya bayyana haka a ranar Litinin a ofishin ƙungiyar da ke Kaduna a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai dangane da wani rubutu da aka yi a shafukan sada zumunta kan naɗin wanda zai zama mataimaki ga Dr Ahmad Gumi wurin gabatar da Tafsiri.
Rubutun wanda ɗaya daga cikin ɗaliban Shaikh Dr. Ahmad Gumi ya yi, ya yi iƙirarin cewa sabon mataimakin mai gabatar da Tafsiri a masallacin, ba mabiyi ne ga makarantar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi ba.
A rubutun, an kuma bayyana cewa, wasu mutane ne da ba su da alaƙa da masallacin da koyarwar Marigayi Sheikh Abubakar Gumi suka yi naɗin mataimakin, don haka ba za su amince da shi ba.
Haka kuma, a cikin rubutun na ɗalibin Dr Gumin, sun jawo hankalin mabiyansu a duk faɗin ƙasar nan da su yi watsi da wannan naɗi na mataimaki da aka yi wa Gumin, inda suka yi zargin cewa, ba a taɓa naɗa wani mataimaki ba, kafin hawan Dr. Gumi kan kujerar.
Don haka, sai ƙungiyar ta Jama’atu ta ce, Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ne da kansa ya sanya hannu a takardar naɗin Dr. Muhammad Jamil Salis a matsayin mataimakin mai tafsiri a wannan masallaci.
“Muna so mu yi cikakken bayani game da naɗa mai Tafsiri a masallacin Sultan Bello. Lokacin da Allah ya yi wa Sheikh Abubakar Gumi rasuwa, Marigayi Sheikh Halliru Binji daga Sakkwato ne aka naɗa domin ci gaba da gudanar da Tafsiri, a ranar 25 ga watan Janairun 1993, har ya amince, amma kafin Azumi ya zagayo, sai Allah ya yi masa rasuwa.
“Bayan rasuwar Farfesa Halliru Binji ne sai aka naɗa Marigayi Sheikh Lawal Abubakar, inda ya kwashe shekaru yana gudanar da Tafsirin, bayan rasuwarsa sai aka naɗa Limamin masallacin Kwalejin Rimi da ke Kaduna, Marigayi Sheikh Umar Hasan.
Bayan ya kwashe kimanin shekaru biyu yana gabatar da Tafsirin, sai aka yi shawarar sanya abin cikin tsari, inda aka naɗa Sheikh Dr. Ahmad Gumi a matsayin wanda zai gudanar da Tafsirin, sakamakon rahoton wani kwamitin da Kanar Hamid Ali ya jagoranta,” in ji Jama’atu.
Don haka, sai Bida ya tabbatar wa duniya cewa, har yana rantsuwa, ba an yi wannan naɗi na mataimakin mai Tafsirin ba ne da wata mummunar manufa, an yi ne don Allah, don ɗaukakar musulunci.
A cewar Malam Bida, an yi wancan rubutun ne da nufin tunzura jama’a da haifar da hargitsi a cikin masallacin da aka daɗe ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Don haka sai Malam Yusuf Bida ya yi ƙarin haske da cewa naɗin Limamai da mataimakansu a masallacin Sultan Bello, haƙƙi ne na Jama’atu, wanda ta daɗe tana yi shekara da shekaru.
Ya ƙara da cewa, bayan an gudanar gwaji na ilimi da sauran fannoni, sai aka cimma matsaya na naɗa wanda ya fi kowa cancanta a matsayin Limami ko mataimakinsa ko mai gabatar da Tafsiri a masallacin. “Da haka ne aka naɗa Shaikh Dr Ahmed Gumi, wanda a yanzu shi ne ke gabatar Tafsiri a masallacin.
Bida ya kuma yi kira ga jami’an tsaro a jihar da hukumar kula da masallacin da su gaggauta ɗaukar ƙwararan matakai a kan duk wani abu da ke ƙoƙarin haifar da rikici a masallacin.