Akalla mutane 61 ne wasu ‘yan bindiga suka sace a kauyen Buda da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
Wani mazaunin kauyen ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 11:45 na daren ranar Litinin, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su tafi da wadanda abin ya shafa.
Mazaunin kauyen wanda ya bayyana sunansa da Dauda Kajuru, ya ce maharan sun yi wa mutanen kawanya kafin daga bisani su sace da dama daga cikinsu.
“Abin da ya faru jiya (Litinin) abin ban tsoro ne. ‘Yan bindigar sun zo ne da nufin sace mutane da dama wanda zai zarce na daliban makaranta a kauyen Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun, amma saurin kawo dauki da sojoji suka yi daga Kajuru, ya taimaka wajen rage adadin wadanda suka sace.
“Yan uwana na cikin wadanda aka sace jiya kuma babu bayanan da muka samu har zuwa safiyar yau,” in ji Manyu.
Ya koka kan yadda aka sauya wani Kwamandan sojoji da aka fi sani da (Tega), wanda ke kokari wajen dakile hare-haren ta’addancin a kauyen.
“Zan fada muku cewa lokacin da Kwamanda Tega yake wajen, hare-haresu ya yi baya, kuma mutum na iya harkokinsa babu fargabar sace shi saboda ya san yanayinsu da kuma yanayin ayyukansu.
“Abin takaici ne dauke Kwamanda Tega daga Karamar Hukumar Kajuru yayin da zaman lafiya ya fara dawowa a kauyukanmu,” in ji shi.
Wani mazaunin yankin mai suna Lawal Abdullahi wanda ya tsallake rijiya da baya amma matarsa na cikin wadanda aka sace, ya tabbatar da sace mutane 61.
Ya ce akwai maza da mata da yara da kuma wata mata mai shayarwa.
“Al’amarin ya tayar min da hankali domin ba mu ji duriyarsu ba tun bayan faruwar lamarin a ranar Litinin.
“Muna kira ga gwamnati da ta dauki mataki kuma ta tabbatar da cewa iyalanmu sun dawo cikin gaggawa,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Mansur Hassan ba amsa kiran wayar da aka masa ba, yayin da gwamnatin jihar kuma ba ce komai game da lamarin ba.