Labarin da muke samu daga majiya ƙwaƙƙwara daga garin Kuriga da aka sace ɗaliban firamare da sakandare na cewa, ‘yan bindigar sun kira waya suna neman a ba su fansar Naira Tiriliyan 1, kafin su sako su.
Har ila yau, majiyar ta tabbatar da cewa, ‘yan bindigar sun bayyana cewa, sun kasa yaran zuwa gida uku, akwai waɗanda aka kai Zamfara, da Neja da kuma dajin Rijana a Jihar Kaduna.
- Juyin Mulki: Sojojin Nijar Sun Fara Shirin Sakin Shugaba Bazoum
- Hukumar Kula Da Wutar Lantarki Ta Kaduna Ta Yi Allah-wadai Da Yajin aikin Ma’aikata
Majiyar wacce ta nemi a ɓoye sunanta saboda dalilai na tsaro, ta ce an sanar da Gwamnatin Jihar Kaduna halin da ake ciki inda Gwamna Uba Sani ya sha alwashin cewa, gwamnatin jihar za ta duba lamarin ta ga abin da za ta iya yi.
Bayani na tafe…