Gwamnatin kasar Sin, ta samar da guraben ayyukan yi na birane da yawan su ya kai sama da miliyan 6.54, cikin watanni shida na farkon shekarar bana.
Alkaluman hukuma sun nuna cewa, adadin ya kai kaso 59 bisa dari, na burin da kasar ta sanya gaba a cikin shekarar.
Ma’aikatar kula da albarkatun al’umma da jin dadin jama’a ta kasar Sin, ta ce yanayin samar da ayyukan yi a kasar ya ci gaba da kasancewa cikin yanayi na daidaito. (Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp