Uwargidan shugaban kasa, Misis Remi Tinubu, ta jaddada cewa, babu wata yarinya da ta cancanci a bar ta a baya wajen samun ilimi sakamakon rauni ko kura-kurai da ta yi a baya.
Ta ce, ya dace a taimaka musu wurin cimma burikansu na rayuwa.
- Mutum 6 Sun Kamu Da Cutar Sanƙarau A Bauchi
- Kasar Sin: Yunkurin Amurka Na Takaita Karfin TikTok Zai Yi Illa Ga Muhallin Zuba Jari Na Kasa Da Kasa
A cewar wata sanarwar da mai taimaka wa uwargidan shugaban kan harkokin yada labarai, ta ce, Uwargidan ta bayyana haka ne a ranar Talata yayin da take jawabi a wurin kaddamar da makarantar koyon sana’o’i ta ‘yan mata da aka gina a jihar Bauchi.
Uwargidan shugaban kasa ta bayyana cewa, ta yi nazarin samar da irin wannan makaranta ne tun tana uwargidan gwamnan jihar Legas, wanda ya kai ga kafa irin wannan a jihar.
Ta kara da cewa, ‘yan mata na iya barin makaranta saboda auren wuri, samun juna-biyu, rashin kudin makaranta da dai sauransu, amma kafa irin wadannan makarantu, ita ce hanyar da ‘yan matan za su gyara kura-kuran da suka tafka na rayuwa.
A jawabinsa a wajen taron, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa, za a ba wa wadanda suka fara cin gajiyar shirin, cikakken tallafin karatu.
Tun da farko dai, uwargidan shugaban kasar, ta kaddamar da wata sabuwar cibiya ta horo kan fasahar sadarwa ta zamani (ICT) a jihar wacce aka sanya wa suna Zainab Bulkachuwa – mace ta farko da ta rike shugabancin kotun daukaka kara ta Nijeriya.