Uwargidan shugaban kasa, Misis Oluremi Tinubu ta bayyana cewar Nijeriya ta shiga yaki da masu garkuwa da mutane.
Misis Tinubu ta bayyana haka ne lokacin da ta karbi bakuncin Sanatocin da ke wakiltar kananan hukumomin Legas uku a ofishinta da ke fadar shugaban kasa a Abuja.
- An Gudanar Da Taron Tattaunawa A Tsakanin Kafofin Watsa Labaru Na Kasa Da Kasa Mai Taken “Sin A Lokacin Bazara” A Amurka
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mata 7 A Wani Sabon Hari Da Suka Kai Kajuru
A cewar wata sanarwa da mai taimaka mata kan harkokin yada labarai, Busola Kukoyi, ta ce Remi ta roki ‘yan majalisar da su samar da dokokin da suka shafi tsaro domin dakile yawaitar garkuwa da mutane.
“Ya kamata mu duba dokokin da za mu kawo. Dangane da batun garkuwa da mutane, mun fara yaki da masu garkuwa da mutane,” in ji ta.
“Gwamnatin shugaban kasa Tinubu ta kuduri aniyar barin tsari ga wadanda ba a haifa ba. Wannan yana bukatar sadaukarwa da jajircewa,” in ji ta.
Tun da farko, jagoran tawagar, Sanata mai wakiltar Legas ta Gabas kuma Shugaban kungiyar Sanatocin Kudu, kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin banki da kudi, Sanata Adetokunbo Abiru, ya bayyana cewa sauye-sauyen da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi za su daidaita tabarbarewar tattalin arziki.
Ya kuma ba da tabbacin cewa majalisar dattawa za ta ci gaba da duba dokokin da suka shafi jama’a, musamman ta fuskar tattalin arziki da tsaro.
Sanata Abiru ya bayyana fatansa na cewa nan ba da dadewa ba al’ummar kasar nan za su fara morar ci gaban tattalin arziki.
Daga cikin wadanda suka ziyarci uwargidan shugaban kasar, akwai Sanata mai wakiltar Legas ta Tsakiya, Wasiu Eshinlokun Sanni wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin sufurin ruwa da kuma Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma, Oluranti Adebule wanda shi ne shugaban kwamitin jin dadin jama’a da yaki da talauci.