Babban taron LEADERSHIP da aka yi kwanan nan ya amsa sunansa, inda aka hada gwaraza wadanda suka yi fice a fannonin bunkasa rayuwar al’umma daban- daban.Taron ya samar da wata dama ta tattaunawa tare da musayar ra’ayoyi a kan yadda Nijeriya za ta ci gaba.
Wasu ra’ayoyin da aka gabatar a wurin taron sun tayar da kura da kuma fito da hanyoyin magance matsalolin da aka fito da su. An kuma gano cewa, musabbabin wasu matsalolin sun taso ne daga tsare-tsaren gwamnati da kuma yadda ake aiwatar da wasu tsare-tsaren.
- Ci Gaban Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
Babban bako mai jawabi a taron, Farfesa Kingsley Moghalu, ya fara daukar hankalin mahalarta taron inda ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar nan na cikin garari, don tabbatar da ikirarinsa ya yi nuni da wasu kurakuran da ke cikin manufofin tattalin arziki na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, a cewarsa wasu manufofin ba a yi cikakken nazari da tunani ba kafin a aiwatar da su. Ya bayar da misalin cire tallafin man fetur da kuma yadda gwamnati ta cire hannu a kan samar wa Naira daraja, da kuma jinkiri da gwamnatin ta yi na nada gwamnan babban bankin Nijeriya da kwamitin da gwamnati ta kafa don lura da tsarin tafiyar da tattalin arzikin kasa musamman ma abin da ya shafi darajar Naira.
A ra’ayinsa, karyewar da tattalin arzikin ya yi zai iya kaiwa shekara uku zuwa biyar kafin ya iya farfadowa. A nasa martanin, Ministan Yada Labarai, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, bai yi wata-wata ba wajen mayar wa da Farfesan da martani, inda ya ki amincewa da bayanin cewar wai tattalin arzikin Nijeriya na cikin garari amma kuma ya yarda da cewa tattalin arzikin Nijeriya yana fuskantar manyan matsalolin da aka dade ba a ga irinsu ba. A ra’ayin Ministan, dukkan matsalolin da ake fuskanta za su wuce a cikin shekara daya ba kamar shekara uku zuwa biyar ba yadda Farfesan ya yi hasashe.
A ra’ayin wannan jaridar, gardamar da ke tsakanin wadannan manyan mutanen a kan wannan lamari da ke da muhimmanci a kan abin da ya shafi jin dadin al’ummar Nijeriya ba shi da wani muhimmanci a kan yadda dukkan su suka yarda da cewa a kwai gaggarumin aiki in har ana son fitar da kasar nan daga cikin halin kuncin da al’ummarta ke ciki.
Ko tattalin arzikin kasa na cikin garari ko kuma yana fuskantar matsaloli babban abin da ya shafi talaka a Nijeriya da ke a gaban sa shi ne yadda zai kai wa bakin salati a kullum in garin Allah ya waye, a daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin tattalin arziki ta fuskoki da dama, ga kuma yadda aka mayar da dala a matsayin jagora a dukkan harkokin saye da sayarwa na kasar nan. Wannan ne ya sa a halin yanzu ake sayar da dala a kan kusan naira 1,500. A kan hakan ko tattalin arzikin Nijeriya na cikin gararin ko kuma yana cikin tsaka mai wuyan wannan ba wani abu mai muhimmanci ba ne ga talakan Nijeriya.
A wannan lokaci lamarin tsaron rayuwa da dukiyoyin al’umma wani abu ne da ke bukatar taimako daga Allah. Wannan ya zama hakan ne domin ‘yan siyasar da kuma jami’an tsaron da ya kamata su dauki matakin kare al’umma sun rasa yadda za su yi kusan basu da wata dabara ta kare al’umma, wannann wani abin kunya ne musamman ganin yadda lamarin yake neman kunyata Nijeriya a idon kasashen duniya.
A halin yanzu kuma a bayyana yake nuna cewa, karancin abinci yana barazana ga al’ummar Nijeriya wanda tuni aka ayyana hakan a matsayin hedikwatar talauci ta duniya, wannan abin takaici ne kwarai da gaske.Wasu kuma na bayyana cewa, a Nijeriya ba wai babu kayan abinci ba ne amma kudin sayen abinci ne suka zama matsala ga mutane, duk dai yadda ka fuskanci lamarin, gidaje da dama na fuskantar matsala a kokarin ciyar da kansu a wannan lokacin da ake ciki. Mutanen ba su damu da abin da ya haifar da matsalar ba, abin da suke fata shi ne al’amurra su dawo daidai yadda ya kamata.
Lamarin wutar lantarki ya kara kazancewa, sauran hanyoyin samun makamashi kuma kamar kalanzir da gas sun zama sai wane da wane. Ba abin da ya shafi su na matsalar da tattalin arzikin Nijeriyan ke fuskanta abin da ake bukata shi ne al’ummarra su dawo yadda aka san su a da.
A shekarar 2023, kungiyar masu masana’antu ta kasa ta bayyana cewa, kamfanoni fiye da 335 suke gab da rufewa yayin da kuma kamfanoni fiye da 767 suka durkushe. Har zuwa yanzu masana na ci gaba da kididdiga tare da tattara alkalumma na marasa aiki a Nijeriya da kuma yadda tattalin arzikin kasa ke kara karyewa a kullum. Suna neman a yi wani abu mai muhimmanci don magance lamarin wanda ba karamin barazana ba ne ga tattalin arzikn Nijeriya.
Mun yarda da ra’ayin Moghalu na cewa, majalisar tarayya ta fi karkata ga biyan bukatun ‘yan siyasa a kudure-kudurenta. A ra’ayinmu lallai ya kamata a yi gyara a wannan lamarin.
A ra’ayinmu, abin da ‘yan Nijeriya ke bukata a halin yanzu shi ne a samar musu da abinci a kan farashi mai sauki.