ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Irin Babban Taron LEADERSHIP ‘Yan Nijeriya Ke Bukata

by Leadership Hausa
2 years ago
LEADERSHIP

Babban taron LEADERSHIP da aka yi kwanan nan ya amsa sunansa, inda aka hada gwaraza wadanda suka yi fice a fannonin bunkasa rayuwar al’umma daban- daban.Taron ya samar da  wata dama ta tattaunawa tare da musayar ra’ayoyi a kan yadda Nijeriya za ta ci gaba.

Wasu ra’ayoyin da aka gabatar a wurin taron sun tayar da kura da kuma fito da hanyoyin magance matsalolin da aka fito da su. An kuma gano cewa, musabbabin wasu matsalolin sun taso ne daga tsare-tsaren gwamnati da kuma yadda ake aiwatar da wasu tsare-tsaren.

  • Ci Gaban Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
  • Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL

Babban bako mai jawabi a taron, Farfesa Kingsley Moghalu, ya fara daukar hankalin mahalarta taron inda ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar nan na cikin garari, don tabbatar da ikirarinsa ya yi nuni da wasu kurakuran da ke cikin manufofin tattalin arziki na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, a cewarsa wasu manufofin ba a yi cikakken nazari da tunani ba kafin a aiwatar da su. Ya bayar da misalin cire tallafin man fetur da kuma yadda gwamnati ta cire hannu a kan samar wa Naira daraja, da kuma jinkiri da gwamnatin ta yi na nada gwamnan babban bankin Nijeriya da  kwamitin da gwamnati ta kafa don lura da tsarin tafiyar da tattalin arzikin kasa musamman  ma abin da ya shafi darajar Naira.

ADVERTISEMENT

A ra’ayinsa, karyewar da tattalin arzikin ya yi zai iya kaiwa shekara uku zuwa biyar kafin ya iya farfadowa. A nasa martanin, Ministan Yada Labarai, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, bai yi wata-wata ba wajen mayar wa da Farfesan  da martani, inda ya ki amincewa da bayanin cewar wai tattalin arzikin Nijeriya na cikin garari amma kuma ya yarda da cewa tattalin arzikin Nijeriya yana fuskantar manyan matsalolin da aka dade ba a ga irinsu ba. A ra’ayin Ministan, dukkan matsalolin da ake fuskanta za su wuce a cikin shekara daya ba kamar shekara uku zuwa biyar ba yadda Farfesan ya yi hasashe.

A  ra’ayin wannan jaridar, gardamar da ke tsakanin wadannan manyan mutanen a kan wannan lamari da ke da muhimmanci a kan abin da ya shafi jin dadin al’ummar Nijeriya ba shi da wani muhimmanci a kan yadda dukkan su suka yarda da cewa a kwai gaggarumin aiki in har ana son fitar da kasar nan daga cikin halin kuncin da al’ummarta ke ciki.

LABARAI MASU NASABA

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

Ko tattalin arzikin kasa na cikin garari ko kuma yana fuskantar matsaloli babban abin da ya shafi talaka a Nijeriya  da ke a gaban sa shi ne yadda zai  kai wa bakin salati a kullum in garin Allah ya waye, a daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin tattalin arziki ta fuskoki da dama, ga kuma yadda aka mayar da dala  a matsayin jagora a dukkan harkokin saye da sayarwa na kasar nan. Wannan ne ya sa a halin yanzu ake sayar da dala a kan kusan naira 1,500. A kan hakan ko tattalin arzikin Nijeriya na cikin gararin ko kuma yana cikin tsaka mai wuyan wannan ba wani abu mai muhimmanci ba ne ga talakan Nijeriya.

A wannan lokaci lamarin tsaron rayuwa da dukiyoyin al’umma wani abu ne da ke bukatar taimako daga Allah. Wannan ya zama hakan ne domin ‘yan siyasar da kuma jami’an tsaron da ya kamata su dauki matakin kare al’umma sun rasa yadda za su yi kusan basu da wata dabara ta kare al’umma, wannann wani abin kunya ne musamman ganin yadda lamarin yake neman kunyata Nijeriya a idon kasashen duniya.

A halin yanzu kuma a bayyana yake nuna cewa, karancin abinci yana barazana ga al’ummar Nijeriya wanda tuni aka ayyana hakan a matsayin hedikwatar talauci ta duniya, wannan abin takaici ne kwarai da gaske.Wasu kuma na bayyana cewa, a Nijeriya ba wai babu kayan abinci ba ne amma kudin sayen abinci ne suka zama matsala ga mutane, duk dai yadda ka fuskanci lamarin, gidaje da dama na fuskantar matsala a kokarin ciyar da kansu a wannan lokacin da ake ciki. Mutanen ba su damu da abin da ya haifar da matsalar ba, abin da suke fata shi ne al’amurra su dawo daidai yadda ya kamata.

Lamarin wutar lantarki ya kara kazancewa, sauran hanyoyin samun makamashi kuma kamar kalanzir da gas sun zama sai wane da wane. Ba abin da ya shafi su na matsalar da tattalin arzikin Nijeriyan ke fuskanta abin da ake bukata shi ne al’ummarra su dawo yadda aka san su a da.

A shekarar 2023, kungiyar masu masana’antu ta kasa ta bayyana cewa, kamfanoni fiye da 335 suke gab da rufewa yayin da kuma kamfanoni fiye da 767 suka durkushe. Har zuwa yanzu masana na ci gaba da kididdiga tare da tattara alkalumma na marasa aiki a Nijeriya da kuma yadda tattalin arzikin kasa ke kara karyewa a kullum. Suna neman a yi wani abu mai muhimmanci don magance lamarin wanda ba karamin barazana ba ne ga tattalin arzikn Nijeriya.

Mun yarda da ra’ayin Moghalu na cewa, majalisar tarayya ta fi karkata ga biyan bukatun ‘yan siyasa a kudure-kudurenta. A ra’ayinmu lallai ya kamata a yi gyara a wannan lamarin.

A ra’ayinmu, abin da ‘yan Nijeriya ke bukata a halin yanzu shi ne a samar musu da abinci a kan farashi mai sauki.

LEADERSHIP
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Gwamnatin Tarayya Na Biyan Tallafin Man Fetur A Asirce – El-Rufai
Siyasa

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

July 16, 2026
M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin  Mataimakinsa
Manyan Labarai

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

July 16, 2026
Next Post
Bayan Sace Dalibai, Mata ‘Yan Hijira Da Almajirai…

Bayan Sace Dalibai, Mata ‘Yan Hijira Da Almajirai…

LABARAI MASU NASABA

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

July 16, 2026
Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

July 16, 2026
Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

Tasirin Da Sabbin Hare-haren Amurka Da Iran Za Su Iya Haifarwa Duniya

July 16, 2026
Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

Sin Na Kokarin Sanya Ci Gaban Fasaha Ya Inganta Bunkasa Da Wadatar Dan Adam

July 16, 2026
Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

Tinubu Ya Miƙa Wa Shettima Takardar Tabbatar Da Shi Abokin Takararsa A Zaɓen 2027

July 16, 2026
Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Kazakhstan

July 16, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.