Ana kallon takardar kudi ta dalar Amurka a matsayin wadda tafi daraja fadin duniya, wadda kuma a yanzu aka fi yin hada-hadar kasuwanci da ita.
Sai dai, takardar dalar ta Amurka, ba ita ce wadda ta fi daraja ba.
- Ci Gaban Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
Kazalika, akwai kuma takardar kudi ta dinar wadda tun a tarihi ake yin amfani da ita a kasar Kuwaiti wadda kuma ta kai sama da kai kashi 180 a cikin dari, da aka fi aminta a matsayin takardar kudi a duniya.
A wani bangare daya kuwa, takardun kudade da ke da rauni wajen yin kasuwanci ita ce takardar kudi ta dala, inda wasu takardun kudaden ke nuna sai an tanadi dubban kudade ne sannan za a iya sayen dala daya kacal.
A nan bari mu yi nazari kan manyan takardun kudade 10 da ke da rauni a duniya sabanin daidai da kan kimarsu, da takardar dala.
Ga jerin manyan takardun kudade 10 da ke da rauni
- Takardar Kudi IRR Ta Kasar Iran
Takardar kudi ta kasar Iran na daga cikin wannan jeren na takardun kudi da ke da rauni a duniya domin da takardar kudi ta Iran daya wato rial, za ka iya sayen dala kacal kan 0.000024 ko kuma ka aje wata dala daya a gefe daya wadda ta kai daidai da takardun kudi na Iran 41,667.
An fara gabatar da takardar kudi ta IRR ne a shekarar 1700 wadda daga baya, ta kai kimar takardar kudi ta Birtniya sai kuma takardar dala ta Amurka.
Amma a yanzu, kudaden da suka fi yawo su na rials, sun kai 42,000 a ‘yan shekarun baya.
Kasar Iran ta kasance a tsakain kogin Gulf da Iraki da kuma Afghanistan kuma ta kasance akan gaba a duniya wajen fitar da mai da kuma gundarin Iskar Gas.
 Sai dai, saboda yawan kakawa kasar takunmi da rigingimu na siyasa da samun hauhawan farashin kaya, hakan ya jefa takardar kudin kasar a cikin mawuyacin hali.
- Takardar Kudi Ta BND Na Kasar Bietnamese:
Takarar kudi ta Dong ta kasar Bietnamese ce ta biyu mai ruani a duniya wadda da ita guda daya za a iya sayen dala 0.000041 ko kuma dala daya da kai daidai da 24,390.
An fara yin amfani da ita ne a 1978 wadda kuma farashinta ke sauya wa daga lokaci zuwa lokaci.
Kasar Bietnam, ta kasance tana da iyaka ne da kojin China na kudu wanda kuma take yin makwbtaka da da Laos da Cambodia. Tana taimakawa tattalin azrkin kasar sai kuma fannonin masana’antu kamar su, m masaku da makamashi.
Kasar ta sha funskantar takunkumi kan zuba jarin kasar waje da kuma dakatar da fitar da kayan da ake sarrafa a cikin kasar zuwa ketare ciki kari da samun akruwar kudin ruwa.
- Takardar kudi ta SLL na kasar Sierra leone:
Takardar kudi ta kasar Sierra Leonean leone, ita ce ta uku mai rauni a cikin takardun kudi na duniya, wanda ta takardar kudi daya z aka iya sayen dala 0.000048 ko kuma dala dya daidai da takardun kudi na kasar da suka kai 20,833.
An fara gabatar da takardar kudin ne a shekarar 1964.
Sierra Leone ta kasance a yammacin Afirak kuma tana da iayka da kasar Guinea da kasar Laberiya.
Kayan da take fitar wa zuwa ketare sun hadada, Timba da ma’adanan kasa kamar su, Gwal Dimond da karafan masana’antu.
Sai dai, kimar kasar ya ragu saboda yadda hauhawan farashin kaya a kasar kai sama da kashi 40 tare da kuma dimbin bashi kari da bullar annobar Ebola da ta bulla a kasar.
- Takardar kudi ta LAK ta kasar Laotian kip:
Takardar kudin kasar ita ce ta hudu mai rauni a duniya, domin da takardar kudi daya ta kasar, za ka iya sayen dala 0.000049 ko dala daya daidai da 20,408.
An fara gabatar da takardar kudin kasar ne a shekarar 1950. Kasar ta kasance a tsakanin kasashen Bietnam da Thailand da Cambodia da kuma China.
Ta dagara ne kan fitar da kaya kamar su, Copper da gwal da Timba. Sai dai, tattalin arzikin kasar ya fuskanci matsala saboda dimbin bashin kasar waje da kuma aukuwar hauhawan farashin kaya, inda hakan ya janyo zubewar darajar takardar kudin kasar.
- Takardar kudi ta IDR na kasar Indonesian rupiah :
Takardar kudin kasar ta rupiah ita ce ta biyar mai rauni a duniya wadda da rupiah daya zaka iya sayen dala0.000064 ko dala daya daidai da 15,385.
An fara gabatar da takardar ta rupiah ce, a shekarar 1946.
Indonesia na da tsubirai da suka kai sama da yawan 17,000 ciki har da Jaba, Sumatra da wani sashe na Borneo da kuma na New Guinea.
Ta kai matsayin babba a kudaici da gabashin Asiya kan karfin tattalin arzikin kasar
 Sai dai, darajar takardar kudin kasar ta fadi saboda samun hauhawan farashi da fada wa cikin matsin tattalin arziki.
- Takardar kudi ta LBP na kasar Lebanese:
Takardar Fam na kasar ita ce mai ta biyar mai rauni a duniya wanda ta takardar daya za ka iya sayen dala 0.000066 ko kuma daidai da Fam daya na 14,925.
An fara gabatar da takardar kudin kasar ne a shekarar 1930 wadda ta kai daidai da darajar dala.
Kasar ta kasance tana da iyaka da kogin Mediterranean haka tana da iyaka da kasashen Isra’ila da Siriya.
Tana da karfin tattalin arziki kuma tana fitar da kaya kamar su duwatsun alfarma da karafa da sanadarai da kayan abinci zuwa ketare.
Karfin takardar ta Fam ya ragu kasa da dala a 2021 saboda lalacewar tattalin arzikin kasar da hauhawan farashin kaya da rashin aikin yi da matsalar da ta shafi bakunan kasar da kuma rikice-rikicen siyasa.
- Takardar kudi ta UZS na kasar Uzbekistani som:
Taktardar kudi ta som na kasar Uzbekistani ta kasance ta bakwai mai rauni wadda takardar ta daya za ka iya sayen dala 0.000081 daidai da dala day ta 12,346 ta som na kasar.
An fara ganbatar da takardar kudin ne a 1993 kuma kasar ta Uzbekistan ta kasance tsohowar jamhuriyyar Sobiet Union wadda kuma ta kasance a tsakiyar Asiya.
Ta kasance kan gaba a duniya wajen fitar da Auduga tana kuma da ma’adanna kasa da mai da kuma da Iskar Gas.
Kasar ta kasance tana wanzar da sauye-sauyen tattalin arzikin ta sai dai, ta ci gaba yin rarrafe kan bunkasar tattalin arzikin ta da rashin aiki yi da kuma fama da cin hanci da rashawa.
- Takardar kudi ta GNF na kasar Guinean :
Takardar kudi ta franc na kasar Guinean ita ce ta takwas a duniya mai rauni wadda da takardar kudin daya, za ka iya sayen dala 0.00012 ko daidai da dala 8,621 na francs.
A fara gabatar da takardar kudin ce a 1959 kasar ta kuma kasance a cikin tsowar kasar Faransa a saharar Afirka.
Kasar na da dimbin ma’adanan kasa kamar su, Gwal da Dimond, amma kasar ta ci gaba da fusktar hauhawan farashin kaya da rikicen-rikicen soji da kwarar bakin haure daga kasashen Liberiya da Sierra Leone.
- Takradr kudi ta PYG na kasar Paraguayan:
Takardar kudi ta guarani na kasar he Paraguayan ita ce ta tara a duniya mai rauni wadda da takardar daya ta guarani, za ka iya sayen dala 0.00014 daidai da dala daya ta 7,463.
An fara gabatar da takardar ce 1952. Kasar ta kaance tana da iyaka ka da kasashen Brazil, Argentina da Bolibia.
Ta kasance kan gaba wajen wajen noman Waken Soya da Rogo da samar da nama kuma tana fitar da Masara da Rake.
Sai dai, hauwan farashin kaya da cin hanci da yawon kudin jabu sun janyo wa tattalin arzikin kasar nakasu.
- Takardar kudi ta UGD na kasar Uganda:
Takardar kudi ta shilling na kasar daya ita ce ta daya mai rauni a duniya wadda ta takardar daya, za ka iya sayen dala 0.00026 wadda ta kai daidai da 3,759. An fara gabatar da ita ne a 1966.
Kasar ta kasance a cikin Afirka ta gabas kuma ta kasance tana da iyaka da kasashen Kenya, Sudan ta kudu, Tanzania da kuma jamhuriyar Congo.
Ta kasance tana da arizkin mai da kuma Gwal da Ganyen coffee sai dai ta ci gaba da fuskantar kalubalen tattalin arziki da dimbin bashi da rikice-rikcen siyasa.