Kungiyar lauyoyi Mata ta kasa (NBA) reshen jihar Adamawa, ta koka da halayyar wasu alkalai da jami’an ma’aikatan kotu a jihar kan cin zarafin mambobin kungiyar.
Duk da dai matan ba su fadi irin cin zarafin da mazan alkalan ke musu ba, amma tuni kungiyar ta kai kara ga babbar alkalin alkalai ta jihar , Mai shari’a Hafsat Abdulrahaman, ta kuma bukaci Mai shari’ar da ta gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda aka samu da laifi.
- PCRC Ta Zabi Sabbin Shugabanni A Adamawa
- Gwamna Fintiri Ya Maka Dakataccen Kwamishinan INEC Na Adamawa, Hudu Ari A Kotu
Barista Fatima Raji Bello, ita ce shugabar Kungiyar Mata Lauyoyi ta Jihar, ta bayyana haka lokacin da su ka kai ziyarar goyon baya ga babbar mai shari’ar, Hafsat Abdulrrahaman, domin tunawa da ranar mata ta duniya a jihar.
Ta ce tuni “Kungiyar ta gabatar da koken cin zarafin da wasu alkalai mazan da jami’an kotuna ga ofsin babbar mai shari’ar.
“Muna kuma bukatar da ku binciki zargin domin ku hukunta duk wadanda ke da hannu a ciki, Muna kira da a horar da dukkan ma’aikatan shari’a kan keta ka’idojin lalata da cin zarafin mata” inji Raji.
Haka kuma shugabar kungiyar ta shaidawa Mai shari’a Hafsat, cewa sun kuma kawo mata ziyarar ne domin jin ta bakinta game da ayyukan da su ka fara a shekarar 2022, sannan ta bukace ta a matsayin uwar Lauya da Bench da su shiga kungiyar ta NBA domin ba su horo da matasa da masu neman zama lauyoyi mata a harkar sana’a a jihar.
Ta kuma yi amfani da ziyarar wajen yabawa babban mai shari’a, Hafsat AbdulRahman da kwamishinan shari’a da kuma babban lauyan gwamnatin jihar, Barista Jingi Afraimu, da ya dauki nauyin lauyoyi 14 domin halartar taro na 2, 3 da 4 na kungiyar matan NBA da aka gudanar a jihar Legas da Abuja.
Da take mayar da martani, babbar mai shari’a, Hafsat Abdulrahaman, ta bayar da hakuri ga duk wani nau’in cin zarafin da alkalai ke yi wa mata lauyoyin, sannan ta yi alkawarin tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ta kuma nuna jin dadi da yadda mata ke samun gagarumin tasiri a kowane fanni na al’amura da sana’o’in da su ka sa a gaba, ta kuma yaba wa alkalai mata musamman wajen yin tasiri sosai kan hukunce-hukunce, tare da bayyana kyakkyawan fata na cewa dandalin Mata lauyoyin zai iya yin abin da ya dace wajen tallafa wa juna.
Mai shari’ar ta kuma yaba tare da godewa shugabanni da mambobin kungiyar bisa wannan ziyara, inda ta bukace su da su kara himma domin aikin lauya ya na bukatar a kula da da’a, kwazon, aiki tukuru da kuma tsafta da ado.