Matashin dan wasan tsakiya dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Amad Diallo, ya bayyana cewar da azumi a bakinsa a lokacin da ya jefa kwallon da ta yi sanadiyar tsallakawar Manchester United zuwa matakin kusa da na karshe na gasar FA Cup.
Diallo wanda ya canji Raphael Varane a minti na 85 ya shigo da kafar dama, inda ya taimakawa Manchester United wajen tsallakawa zuwa matakin kusa da na karshe a mintunan karshe na wasan.
- Harsashen Abun Da Zai Iya Faruwa A Wasan Manchester City Da Liverpool Na Yau
- Watakila Rashford Ya Bar Manchester United
Bayan kammala mintuna 90 na wasan ba tare da wata kungiya ta samu nasara ba, alkalin wasa John Brooks ya kara mintuna 30 inda Harvey Elliott da Marcus Rashford kowa ya jefa kwallo daya.
Kwallon da Diallo dan asalin kasar Cote de’Voire ya zura a minti na 120 yasa Manchester United ta tsallaka zuwa matakin wasan kusa da na karshe na gasar FA, inda zata hadu da Coventry City.