A ranar 15 ga wata, an cika shekaru biyu da tsai da ranar 15 ga watan Maris na kowace shekara a matsayin “ranar duniya ta adawa da kyamar musulunci”. A gun taron MDD na tunawa da ranar da aka gudanar, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing ya gabatar da jawabi, inda ya jaddada cewa, ‘yancin fadin albarkacin baki ba zai iya kare wadanda suka yi kalaman nuna kyama ba, ballantana ma ya zama dalilin gwamnati na rashin daukar matakai.
A cikin ‘yan shekarun baya, sakamakon tsanancewar rikicin siyasa a tsakanin sassan duniya, wasu ’yan siyasar kasashen yammacin duniya na ta kara tunzura fito na fito tsakanin al’ummu da wayewar kansu. Idan ba a manta ba, sau da dama, wasu tsirarrun ’yan siyasar Turai sun kona Alkur’ani mai tsarki a fili. A bara, yayin da al’ummar musulmi a sassan duniya suka yi shagulgulan babbar sallah, wani abu da ya faru a Turai ya bata yanayin bikin, inda bisa amincewar ’yan sandan wurin, an sake samun wani da ya kona Alkur’ani mai tsarki a wajen wani masallacin da ke birnin Stockholm, babban birnin kasar Sweden. Bayan aukuwar lamarin, kakakin majalisar harkokin wajen Amurka Matthew Miller da ma babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, duk sun bayyana cewa, wannan na daga cikin ’yancin jama’a na fadi albarkacin bakinsu. Sai kuma a watan Janairun shekarar 2017, gwamnatin kasar Amurka ta kaddamar da dokar kayyade shigar da al’ummar kasashen musulmi kasar, matakin da ya sa ta zama kasa daya tilo a duniya da ta sanya haramci kan rukunin al’ummar musulmi. Sai kuma mujallar Charlie Hebdo ta Faransa ta sha wallafa zanen barkwanci da suka tada sabani a tsakanin addinai da kabilu daban daban. Duk wadannan lamura sun tunzura kiyayya a tsakanin mabambantan al’ummu, tare da tsananta rashin fahimtar juna a tsakanin kabilu daban daban, kuma ainihin dalilin da ya sa haka shi ne yadda kasashen yammacin duniya ke nuna bambanci ga irin al’ummun da ba nasu ba, wadanda a ganinsu, wayewar kai na yammacin duniya ya fi na sauran sassan duniya.
- Shugaba Xi Jinping Ya Taya Shugaba Putin Na Kasar Rasha Murnar Lashe Zabe
- Xi Ya Ba Da Umurni Kan Gobarar Da Ta Faru A Birnin Xinyu Na Lardin Jiangxi
Ranar 15 ga wata ta kuma cika shekara daya da kasar Sin ta gabatar da shawarar kiyaye mabambantan wayewar kan duniya, wato Global Civilization Initiative a Turance. Kasancewar kasar Sin kasa ce da ta dade tana samun mabambantan kabilu da addinai da wayewar kai da dama, tana rike da ra’ayi da ya sha bamban sosai da kasashen yamma ta fannin wayewar kan kasashe da kabilu daban daban, wadda a ganinta, duk da bambance bambance da ke tsakanin wayewar kai iri iri, amma babu wani da ya fi wani na daban, don haka ma, kullum take kira da a kiyaye kasancewar mabambantan wayewar kai, tare da sa kaimin yin musaya a tsakaninsu. Sabo da irin wannan akidar martaba mabambantan wayewar kai da kasar Sin ke da shi, a watan Maris na bara, kasar ta gabatar da shawarar kiyaye mabambantan wayewar kai a duniya, inda ta yi kira da a aiwatar da manufofin daidaito, da koyi da juna, da tattaunawa, da tafiya tare tsakanin dukkanin wayewar kan al’ummun duniya, shawarar da ta samu karbuwa daga akasarin kasashen duniya.
A gun wani taron kara wa juna ilmi dangane da shawarar da aka gudanar a farkon bana, mataimakin shugaban jami’ar Abuja Dr. Abdul-Rasheed Na’Allah ya ce, tabbas shawarar za ta samar da kuzari wajen sa kaimin zamanintar da harkokin ‘yan Adam da ma gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Kasancewarta kasa mafi yawan al’umma da ma mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, Nijeriya ma na kan hanyar zamanintar da kanta. Dr. Abdul-Rasheed Na’Allah ya ce, “Nijeriya na bukatar yin koyi da mabambantan wayewar kai wajen bunkasa kanta, amma dole ne mu fahimci cewa, ba dole ba ne mu koyi komai daga kasashen yamma domin zamanintar da kanmu.” A ganinsa, ma’anar shawarar nan ita ce ta bayyana wa duniya cewa, kasa da kasa na da ‘yancin zabar tsarin da ya dace da yanayinsu, a yayin da suke da ‘yancin kiyaye al’adun gargajiyarsu.
Akwai kasashe da yankuna sama da 200 a duniyarmu, inda ake samun kabilu sama da 2500, wadanda sabo da bambancin tarihinsu da yanayin kasashensu, suka haifar da mabambantan wayewar kai, kuma hakan ya kara kyautata duniyarmu.(Lubabatu)