Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya amince da kashe naira biliyan 1 domin horas da malaman makarantun firamare a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.
Zulum ya sanar da amincewar ne a ranar Talata a Maiduguri yayin da yake kaddamar da sabbin sakatarorin ilimi na kananan hukumomi da aka nada wadanda za su gudanar da harkokin ilimin firamare a kananan hukumominsu.
Gwamnan ya bayyana cewa, fiye da malamai 1,000 da ke da takardar shedar karatu ta OND za su kara samun horon koyarwa.
Horon, a cewar Gwamnan, zai shafi malaman da ba su da shaidar karatun koyarwa amma an same su da su da kwarewa kan karantarwa kamar yadda bayanan gwajin cancantar koyarwa da aka yi musu ya nuna.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa, gwamnatinsa a shekarar 2019, lokacin da aka rantsar da shi, ta fara sake gina gine-ginen makarantu da suka lalace, hakan, a cewarsa ya haifar da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta zuwa 800,000 daga fiye da miliyan biyu.
Gwamnan ya bukaci sabbin sakatarorin ilimi da aka nada da su sauke nauyin da ke kansu yadda ya dace, ya kuma yi gargadin cewa duk wanda aka samu da gazawa za a maye gurbinsa.