A wani babban mataki na rage tsadar mulki, Shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar hana tafiye-tafiye na tsawon watanni uku zuwa kasashen waje da ake amfani da kudaden gwamnati ga duk ministoci, shugabannin hukumomin gwamnati, da sauran jami’ai.
Haramcin, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, 2024, an yi shi ne don rage yawan amfani da kudade da ma’aikatu, sassan gwamnati, da hukumomin (MDAs) ke kashewa kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da kuma tabbatar da cewa ma’aikatan MDAs sun mai da hankali kan ayyukan da ya rataya a kansu.
- Kotu Ta Daure Barawon Alkur’ani Watanni 15 A Abuja
- Da Dumi-Dumi: Majalisa Ta Amince Da Kudirin Bai Wa Dalibai Bashi
Wannan umurnin na kunshe ne acikin wata wasika mai kwanan wata 12 ga Maris, 2024, mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, kuma aka aika zuwa ga sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
Haramcin wani bangare ne na kokarin da Tinubu ke yi na rage kashe kudade da gwamnati ke kashewa da kuma inganta tsarin kashe kudi.