Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Harry Kane ya kafa tarihin yawan cin kwallo 31 a gasar bundes liga ta kasar Jamus, bayan da Bayern Munich ta je ta doke Darmstadt 5-2 a Bundesliga.
Hakan ya sa Bayern Munchen ta rage tazarar makin dake tsakaninta da mai jan ragamar teburi, Bayern Leberkusen yanzu ya koma saura goma bayan da itama Bayern Lib-erkusen din ta samu nasara a wasanta. Darmstadt ce ta fara cin kwallo ta hannun Tim Skarke daga baya Jamal Musiala ya farke, Kane ne ya ci wa Bayern ta biyu, sannan Musila ya kara ta uku ta biyu da ya zura a raga a fafatawar.
- An Yi Nasarar Gudanar Da Dandalin Jihar Legas
- Hedkwatar CDC Ta Afirka Ta Samu Yabo A Matsayin Babban Sakamakon Hadin Gwiwar BRI
Dan wasa Serge Gnabry da Mathys Tel ne suka ci wa Bayern Munchen sauran kwal-laye da suka cika biyar a ragar, sai Oscar Bilhelmsson ya sake zare daya a wasan da aka doke Darmstadt 5-2 a fafatawar ta Bundesliga.
An yi fargabar ko Kane, dan wasan tawagar Ingila ya ji rauni a zagaye na biyu, bayan da ya yi karo da turken raga, sannan an canja shi saura minti takwas a tashi a wasan kuma kociyan Bayern, Thomas Tuchel bai yi karin bayani ba kan girman raunin tsohon dan wasan Tottenham din ba.
Kane ya taba cin kwallo 30 a kakar wasa a lokacin da yake Premier League a Totten-ham sannan kuma ya kafa tarihin zura kwallaye da yawa a Bundesliga a kakarsa ta far-ko, wanda ke rike da tarihin shi ne Uwe Seeler mai 30 a kungiyar Hamburg a 1963 zu-wa 1964. Zai ziyarci Ingila a gasar Champions League zagayen kwata fainals a
karawa tsakanin Bayern Munich da Arsenal – ya ci kwallo 14 a wasa 19 da ya fuskanci kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.
Bayern Munich za ta fara zuwa filin wasa na Fly Emirates ranar 9 ga watan Afirilu, su buga fafatawa ta biyu a Jamus ranar 17 ga watan Afirilu.