Kungiyar kwallon kafa ta Fc Barcelona ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai (UEFA) ta bana bayan tashi wasan da ta sha kashi a hannun Borrusia Dortmund da ci 3-1 a Signal Iduna Park.
Kadan ya rage wankin hula ya kai yaran na Flick dare, yayin da Seihou Guirasy ya jefa kwallaye uku rigis a ragar Scezesny, wannan shi ne karon farko da Barcelona ta yi rashin nasara a wasanninta na shekarar 2025.
- Minista Ya Gargaɗi Jami’an Gwamnati Kan Rashin Sanin Ilimin Tantance Ingantattun Labarai
- An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin shekaru 2 A Gidan Yari Saboda Yunƙurin Daɓa Wa Mahaifinsa Almakashi A Kano
A wasan farko dai Barcelona ce ta doke abokiyar karawarta Borrusia Dortmund da ci 4-0 a filin wasa na Luis Companys da ke birnin Barcelona, amma kuma Dortmund da ake wa lakabi da Black And Yellow ta so ta jikawa Barcelona aiki a daren ranar Talata.
Da wannan sakamakon na 5-3 a duka wasannin biyu Barcelona ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na karshe a karon farko tun a shekarar 2016 da su ka buga wasa a wannan matakin na gasar Zakarun Turai tare da Athletico Madrid.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp