• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dole Ne Mu Ajiye Bambancin Addini, Ƙabilanci Da Siyasa A Baya – Ministan Yaɗa Labarai

by Sulaiman
2 years ago
Labarai

Wata tabbatacciyar hanya ta samun haɗin kan ‘yan kasa, itace sanya bambancin ƙabilanci, addini, da siyasa a baya, hakan zai samar da ƙarfafa amana da amincewa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai ga ministan yada labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya ce, Minista Muhammad Idris ya bayyana muhimmancin sanya banbancin dake tsakanin ‘yan kasa a baya domin samun nagartacciyar kasa a yayin da yake jawabi a taron farko na masu magana da yawu wanda Cibiyar Hulɗa Da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta shirya tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta Tarayya a ranar Talata a Abuja.

  • Sojoji Sun Wanke Fursunoni 200 Da Ake Zargin Alaka Da Boko Haram A Borno
  • Masu Satar Mutane Za Mu Dauke Su A Matsayin ‘Yan Ta’adda – Tinubu

Da yake jawabi kan taken taron, wato “Canza Labari, Canza Al’umma”, ministan ya ce, bisa la’akari da bambance-bambancen da Nijeriya take da shi, akwai buƙatar a samar da haɗin kan ƙasa wanda ya zarce ƙabilanci, addini, da siyasa ta hanyar ƙirƙiro da labari mai ban sha’awa na ƙasa, wanda ke ƙarfafa amana da amincewa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Ya ce babban gangamin wayar da kan jama’a na ma’aikatar sa mai taken “Kundin Tsarin Ɗabi’un Nijeriya” wanda nan ba da daɗewa ba Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar da shi, ya ƙunshi yarjejeniyar zamantakewa tsakanin ƙasar da ‘yan ƙasar, kuma zai kasance wani shiri na tsarin ɗabi’un ƙasa wanda ke bayyana ‘yan Nijeriya da kuma ƙarfafa halayen su a matsayin su na ’yan ƙasa.

Idris ya ce, “Abu na musamman game da wannan Kundin Ɗabi’un shi ne yarjejeniya ce ta zamantakewa tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa kuma tana ɗauke da Manyan Wajibai Bakwai na ƙasar Nijeriya ga ‘yan ƙasa da kuma Alƙawura Bakwai na ‘yan ƙasa ga da ƙasar su. Jigon Kundin Ɗabi’un shi ne dole ne gwamnatin da zaɓaɓɓu da naɗaɗɗun wakilai ke wakilta ta cika wasu muhimman alƙawura don samun muhimman alƙawura daga ‘yan ƙasa.”

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

Haka kuma ya yi tsokaci kan amana a matsayin ginshiƙin hanyar sadarwa mai inganci kuma mai ɗorewa, yana mai cewa yayin da makomar sadarwa ke nuni ga fasaha, fasahar za ta iya yin tasiri mai ma’ana ne kawai idan aka ɗora ta kan amana.

Ya ce: “Amana ta kasance muhimmin abu wajen gina dangantaka; na kai, na ƙungiya, har ma da na al’umma.

“A matsayin mu na masu magana da yawu, muna buƙatar mu yi ƙoƙari na gaske don gina amana da maido da fata tagari a duk inda muke. Dole ne ginawa da kiyaye amana ya zama wani nauyi da ya rataya a wuyan kowa.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro
Manyan Labarai

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro

October 27, 2025
Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina
Labarai

Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina

October 27, 2025
Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?
Ra'ayi Riga

Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka?

October 27, 2025
Next Post
Xi Jinping: Ya Kamata Bangarori Daban Daban Na Sin Da Amurka Su Kara Mu’amala Da Fahimtar Juna

Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba

Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 

October 27, 2025
An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Labarai

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.