Ranakun 25 ga watan fabrairu da 11 ga watan Maris shekarar 2024, sun zama ranakun da suke tuna wa ‘yan Nijeriya lokacin da aka gudanar da zabuka masu cike da tarihi a kasar nan.
Wadannan ranakun ne da aka gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun kasa da kuma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
- Azumi Lokaci Zafi: Yadda ‘Yan Kasuwar Kankara Ke Camamarsu A Yobe Da Zamfara
- Jimilar Kudin Da Sin Ta Samu Wajen Jigilar Kayayyaki A Farkon Watanni Biyu Na Bana Ta Kai Yuan Triliyan 55.4
Zabukan sun kasance masu muhimmancin gaske, kasancewar ana gudanar da gwamnatin farar hula na tsawon shekaru 24 ba tare da katse ba, ma’ana sojoji ba su amshi mulki ba, kuma karo na farko a tarihin Nijeriya tun bayan samun mulkin kai. An dai samu masu saka ido na cikin gida da kuma kasashen ketare da wadannan zabuka.
Mafi yawan masu sanya idanu sun bayyana cewa zaben 2023 shi ne mafi tsada a Nijeriya, inda ya lashe makudan kudade sama da naira biliyan 355 tun daga buga takardun jefa kuri’a har zuwa hidindimun da aka gudanar a lokacin zaben da kuma bayan zaben.
Duk da an sami karin rajistar masu zabe har miliyan 10 bayan a baya ana da miliyan 84, an sami karancin fitowar masu jefa kuri’a.
A shekarun da suka gabata, an yi kokarin kauce wa wasu matslaolin zabe da ake samu kamar satar akwati da tarwatsa wajen zabe da wasu bata-gari ke yi da saye da sayar da kuri’a da matsalar tsaro da karya dokokin zabe da wasu jam’iyyu ke yi wajen tsayar da dan takara.
A batun gaskiya, zaben da aka gudanar a wasu yankuna a watan Nuwamba na shekarar 2023, ya sanya an gano wasu kura-kurai da jam’iyyun siyasa suke tafkawa, wanda ya zama izina ga hukuma da su kansu jam’iyyu. Hakan ta za aka dauki mataki a zaben gwamnonin da za a gudanar a jihohin Edo da Ondo a shekarar 2024.
Zaben 2023 ya zo da wasu kalubale da suka hada da fargaban rashin tsaro da matsalar tattalin arziki da talauci da ya addabi al’umma ta ko’ina, wanda ya hade da burukan ‘yan siyasa da suke neman madafun iko ta kowani hali.
Kafin lokacin zaben, wasu abubuwa sun kara bayyana kamar kabilanci da bangaranci da bambance-bambancen addini, wanda wadannan dalilai suna daga cikin abubuwan da suka sanya aka sami karancin masu fitowa zabe.
Haka kuma zaben 2023, an sayi kuri’u masu yawan gaske, inda ‘yan siyasa suka rika bai wa al’umma kudi da kyaututtuka, wadannan abubuwan sun shafi kima da darajar zaben matuka don sun yi tasiri sosai.
Baya ga wadannan kuma, wasu malaman addini da masana sun rika amfani da damarsu wajen kira da a zabi wasu bangare, wanda wannan ma ya saba wa tsarin dimokuradiyya. Amma a hannu guda kuma, wasu malaman da masana harkokin rayuwa sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar zaben 2023.
Hukumar INEC wacce a halin yanzu take shirin gudanar da zabukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo ba tare da an sami matsaloli ba kamar yadda aka samu a zaben gwamnonin jihohin Kogi da Imo da Bayelsa a kwanakin baya, ta ja hankalin jam’iyyun siyasa wajen ganin sun iya abun da ya dace bisa tsarin doka.
Sanin kowa ne a duk inda za a yi zabe a duniya ba wai a Njeriya ba, ba a rasa wasu matsaloli daga nan zuwa can. Amma a nan Nijeriya babban abun da ake bukata shi ne, hukumar INEC ta yi kokarin yin adalci wajen ayyukanta, yin haka ne kawai zai tabbatar da dorewar dimokuradiyya.
Sannan hakan ne zai sa al’umma su rika fitowa yin zaben, domin suna da tabbacin za a ba su abun da suka zaba, kuma za a tsare masu rayukansu.
Alamu dai na nuna cewa har yanzu dai a bangaren zabe, Nijeriya ba ta tsaya da kafafunta ba.