Sakamakon yin azumi a lokacin bazara da kuma karancin wutar lantar a Nijeriya ya sa ‘yan kasuwar kankara ke camamarsu a bana.
A Jihohin Borno da Yobe suna daga ciki bangarorin kasar nan da ke gaba-gaba a tsananin zafin rana, sakamakon yadda suke da adadin murabba’in daruruwan kil-omitoci da sahara ta mamaye a Arewa Maso Gabashin Nijeriya kuma sun yi iyaka da Jamhuriyar Nijar, Chadi da Kamaru.
Yanayin zafin ranar yankin ya bambanta da na sauran yankuna tare da guguwa mai dauke da iska mai zafi a lokacin bazara. Haka zalika, yanki ne mai karancin bishiyoyi masu inuwar da mutum zai sarara, face kebantattun wuraren da suke gabar Kogin Kumadugu da makamantan sa.
- Ce-ce-ku-ce Ya Barke Tsakanin PDP Da APC Kan Zargin Kama Mambobi 25 A Osun
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Benin Domin Tattauna Hanyoyin Karfafa Dangantakar Kasashensu
Yanki ne wanda sakamakon matsalolin tsaron da ya sha fama da su, har yanzu al’ummar yankin ba su kammala fita daga cikin tasku da matsin rayuwa da rikicin Boko Haram ya jefa su a ciki ba. Al’amarin da ya shafi kusan kowane fannin jin dadin rayuwa, inda maharan suka rinka rusa manyan layukan wutar lantarkin da ya sada manyan biranen jihohin Maiduguri da Damaturu ba su da lantarki.
Bugu da kari, birnin Maiduguri ya kwashe watanni ba tare da wutar lantarki ba, sakamakon ayyukan ‘yan kungiyar Boko Haram da suka katse manyan layukan wutar lantarki tun a bara, duk da matakin da gwamnati ta dauka na gyara amma dai ba ta canja zani ba.
Haka abin yake a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, wanda a cikin kasa ga katanni hudu, Boko Haram sun katse layukan wutar lantarkin da ke baiwa jihohin biyu wutar lantarki a kauye Kasesa dake daf da Damaturu.
Wadannan sun jawo samun ruwan sanyi ko kankara don sanyaya makoshin masu azumi ya wuyata. Wanda hakan ya jawo tsadar kankara tare da sauran abu-buwan sanyi wadanda mai azumi yake bukata domin sanyaya makoshi a lokacin buda baki.
Jama’a da dama sun shaida wa LEADERSHIP cewa yanzu haka su na sanyen kankarar ‘Pure Water’ daya kan 200 ko 150 a wadannan manyan garuruwa da makamantan su.
Malama Fatima Mustapha, mazuniyar birnin Maiduguri ta bayyana cewa, “Tun shigowar azumin haka muke ta fama da tsananin zafi sakamakon rashin wutar lantarki, wanda tun bayan shigowar watan Ramadan ba mu samu isasshen wutan ba, alhalin ga azumi ga tsanain zafin da ake da shi a nan Borno.
“Wanda hakan ya tilasta dole sai mutum ya yi tafiya mai nisa zuwa wasu ungu-wanni kafin ya samu kankara, kowace ake sayar da ledar Pure water daya kan 200. Sannan ga yanayin matsin rayuwa.”
A nashi bangaren kuma, Malam Abubakar Usman Damaturu, ya bayyana cewa rashin samun isasshen wutar lantarki a birnin shi ne ummul-haba’isan tsadar kankara tare da sauran kayan masarufi.
“Mafi yawan kankarar ana kawota ne daga Potiskum, wanda a farkon azumi kowace daya 500 ce (ba ta pure water ba). Sannan kuma zancen wutar lantarki kam sai dai mu ce Alhamdulillah.” In ji shi.
A Jihar Zamfara ma haka lamarin yake, domin kuwa al’ummar Jihar Zamfara al’umar na matukar shan wahala a wannan azumi wajen sanyaya makoshi a loka-cin buda baki.
Wannan ne ya sanya wasu su ka yi wa sana’ar sayar da kankara kutse ganin yad-da farashin ke hauhawa, musamman a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.
Hamza Zurmi ya bayyana wa wakilinmu cewa, dafifi magidajan ke yi wajen sayan kakara ga layi mai tsawo duk da kuwa ba kowane yake samun yadda yake soba.
A yankin Janyau ta gabas da Samaru Gusau, a wani ashirin da hudu suke yi kan samun wuta lantarki, inda ake matukar shan wahala tare tsadar wajen sayen kankara.
Masu sayar da kankara a azumin bana sun yi camamarsu a mafi yawancin yankunan kasar nan sakamakon tsananin zafi da kuma rashin samun isasshin wutar lantarki.