Shahararren malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana makasudin gayyatarsa ofishin hukumar tsaro ta farin kaya, wanda ya ce an gayyace shi ne domin kawo mafita ga matsalar ‘yan bindiga a kasar nan, musamman ma a yankin arewa.
Gumi ya kara da cewa gayyanatar nasa yana da mutukar muhimmanci, domin ya samu nasarar tattaunawa da jami’an tsaro.
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Benin Domin Tattauna Hanyoyin Karfafa Dangantakar Kasashensu
- Sojoji Sun Hallaka Kasurgumin Dan Bindiga, ‘Junaidu Fasagora’ Da Yaransa A Zamfara
Sai dai a ranar Litinin, ministan yada labarai, Mohammed Idris ya tabbatar da cewa an gayyaci Sheikh Gumi ne domin amsa tambayoyi kan furucinsa game da ‘yan bindiga a kasar nan. Ya kuma bayyana cewa lallai babu wanda ya fi karfin doka.
Da yake mayar da martani a safinsa na kafar sada zumunta, Sheikh Gumi ya rubuta cewa, “Mutum daya ne kadai ya fi karfin doka, shi ne mara laifi. A jiya na samu ki-yan waya mai yawa daga ‘yan jarida kan cewa jami’an tsaro suna tuhumata.
“Gaskya ne mun tattauna da jami’an tsaro yadda za a iya shawo kan matsalar ‘yan bindiga a cikin fadin kasar nan. Babu wani cin zarafina, sai dai mun gana cikin mu-tuntawa.
“Muna bukatar hadin kai a kasar nan wajen yin aiki tare domin samun nasarar kawo zaman lafiya. Ina mai gode muku kan nuna min kauna. Ina rokon Allah ya ci gaba da dafa mana a kowani lokaci. Amin,” in ji Gumi.