Majalisar dokokin Isra’ila ta kada kuri’ar amincewa da korar kafar talibijin ta Al Jazeera daga cikin kasar, sakamakon sha’anin tsaro.
Wannan na zuwa ne, bayan da ministan yada labaran kasar, Shlomo Karhi ya sanar da cewa nan da ‘yan kwanaki za a rufe duk wani ofishin Al Jazeera da ke kasar.
- Lokaci Ya Yi Da Kasashen Yamma Za Su Yi Watsi Da Tunanin Wai Sun Fi Sauran Kasashe
- Saurayi Ya Raunata Budurwa Tare Da Barazanar Kisa Saboda Ta Ki Son Sa A Maiduguri
Tuni dai Firaminista, Benjamin Netanyahu ya yi maraba da matakin majalisar dokokin kasar, inda ya bayyana cewa, lokaci ya yi da ya kamata Al Jazeera ta daina daukar labarai daga Isra’ila.
Gidan talibijin din mai hedikwata a birnin Doha na kasar Qatar, ya bayyana cewa, tun da farko an yi barazanar yin amfani da matakan gaggawa don rufe ofisoshin Al Jazeera a Isra’ila da yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
A tsakiyar watan Oktoban 2023, gwamnatin Isra’ila ta zartar da manufofin da za su ba ta damar rufe kafafen yada labaran kasashen waje na wani dan lokaci.
Isra’ila dai na yi wa gidan talabijin na Al Jazeera kallon babban barazana ga yakin da ta ke yi da Falasdinawa da kuma tsaro ga kanki kanta.
A shekarar 2022 da ma irin wannan mataki ya taba faruwa a Afghanistan lokacin da Taliban ta karbe ikon mulkin kasar, tare da korar gidajen talabijin na kasashen waje ciki har da Al Jazeera.