• English
  • Business News
Saturday, June 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Yanar Gizo Na Kyautata Rayuwar Jama’a

by CGTN Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Hadin Gwiwar Afirka Da Sin A Fannin Yanar Gizo Na Kyautata Rayuwar Jama’a
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Abokaina, bari mu yi tunanin abkuwar wani batu: A cikin wani kauye dake wata kasa ta nahiyar Afirka, wani yaro ya kamu da zazzabi da tsakar dare, amma likita ba zai samu damar zuwa gidan yaron cikin gaggawa ba, saboda yana zaune a cikin gari. Amma iyayen yaron ba su damu ba, maimakon haka sai suka bude wata manhaja (APP) dake cikin wayar salula, da rubuta bayanin halin da yaron ke ciki kan APP din. Sa’an nan bayan kimanin minti 10, sai wani karamin jirgin sama maras matuki ya sauka a gaban kofar gidansu, dauke da maganin da yaron ke bukata.

Hakika wannan batun da muka yi tunani ya riga ya zama gaskiya. Wani saurayi dan kasar Zambia mai suna Clivate Maiba ya koyi dabarar amfani da dandalin sarrafa na’urorin zamani a kasar Sin, sa’an nan ya bude wani kamfanin samar da hidimar jinya a kasarsa ta Zambia, inda ake gwada yin amfani da fasahar zamani wajen sarrafa jirgin sama maras matuki, don kai magani, da jini, da alluran rigakafi da ake bukata, ga likitoci da daidaikun mutane da ke zama a yankunan karkara marasa hanyoyi masu inganci.

Wannan misali ya nuna yadda hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin ta fuskar yanar gizo ko Internet da fasahohin zamani ke haifar wa matasan kasashen Afirka damammakin kaddamar da sabbin sana’o’i, sa’an nan an samar da taimako ga masu raunin tattalin arziki dake nahiyar Afirka a fannin kyautata zaman rayuwarsu.

  • Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Mai Inganci A Manyan Bangarori 5

A yau Talata an gudanar da wani dandalin tattauna damar hadin gwiwa kan ci gaban yanar gizo ko Internet, tsakanin bangarorin Afirka da Sin, a birnin Xiamen na kasar Sin, inda jami’ai da ‘yan kasuwa na bangarorin 2 suke mai da hankali kan damar hadin kansu, a fannonin tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani, da kafofin yada labaru na yanar gizo, da tsaron yanar gizo, da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, da dai sauransu, gami da tattauna dabarar yin amfani da yanar gizo da fasahohin zamani wajen kyautata zaman rayuwar jama’a, kamar dai yadda misalin kasar Zambia da na gabatar muku ya nuna.

Cikin shekarun nan, an samu dimbin nasarori a hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, a fannin yanar gizo ko Internet. Misali a bangaren gina kayayyakin more rayuwa, ya zuwa karshen shekarar 2021, kasar Sin ta gina fiye da kashi 50% na tashoshi da yanar gizo mai sauri na wayar salula, gami da shimfida kananan wayoyin aika sako ta haske fiye da tsawon kilomita dubu 200, a kasashen Afirka. Kana a fannin ciniki ta yanar gizo, sama da rabi na yawan cinikayyar yanar gizo da ake yi a kasuwannin gabashin Afirka an yi su ne ta dandalin ciniki na Kilimall da wani basine ya kafa, inda yawan mutanen da suke amfani da dandalin ya zarce miliyan 10. Sa’an nan a fannin hada-hadar kudi, kamfanin Opay na kasar Najeriya ya shigar da jari da fasahohi daga kasar Sin, ta yadda ya zama daya daga cikin kamfanonin hidimar biyan kudi mafi girma a kasar Najeriya. A sauran fannoni irinsu horar da ma’aikata, da tsaron yanar gizo ma, ana samun yanayi kusan iri daya. Za a iya cewa a kusan dukkan sana’o’i masu alaka da fasahohin yanar gizo na galibin kasashen dake nahiyar Afirka, ana iya ganin yadda fasahohi da jarin kasar Sin ke taka muhimmiyar rawa.

Labarai Masu Nasaba

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

Za a so a yi tambaya cewa, me ya sa kasar Sin ce ke taka rawa a fannin? Kuma don me ake son hadin gwiwa da kasar Sin, yayin da ake neman raya sana’o’i masu alaka da yanar gizo ko Internet?

Dalilin shi ne, da farko, fasahohin kasar Sin a fannin yanar gizo su ne a kan gaba a duniya.

An kammala aikin gina kayayyakin more rayuwa masu alaka da fasahohin sadarwa mafi girma a duniya, a kasar ta Sin, ta yadda ko a cikin kauyukan kasar ma, ana samun ingantaccen tsarin sadarwa. Ban da haka, kasar ita ta fara rungumar fasahar sadarwa mai ci gaba ta 5G, inda a karshen shekarar 2023, yawan al’ummar kasar masu wayoyin salula dake aiki da 5G ya kai miliyan 805. Ban da haka, kasar Sin ta kware a fannin kirkirar sabbin fasahohi, abin da ya sa ta kan gaba a duniya a fannonin mallakar fasahohi masu alaka da na’urorin kwaikwayon tunanin dan Adam, da aikin tsara karamin kayan latironi na Chip, da dai sauransu.

Kana dalili na biyu shi ne, akidar kasar Sin ta fuskar hadin kai tare da kasashen Afirka ta gaskiya, da kauna, da sahihanci, gami da samar da sakamako na zahiri, ta sa kasar yarda da gabatar da ingantattun fasahohi, da damammakin raya kasa, ga bangarorin Afirka. Cikin shawarar kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin yanar gizo bisa hadin gwiwar Sin da Afirka, da kasar Sin ta gabatar, kasar ta yi alkawarin taimakawa kasashen Afirka wajen gina kayayyakin aikin sadarwa, da kula da yanar gizo, da sayar da kayayyaki ga kasuwannin Sin ta hanyar cinikin yanar gizo, da kuma rage talauci ta hanyar amfani da fasahohin zamani.

Idan muka leka kasar Sin, za mu ga yadda yanar gizo ko Internet ta shafi dukkan bangarorin rayuwar jama’ar kasar, irinsu sayayya, da biyan kudi, da hulda da abokai, da karatu, da ganin likita, da gudanar da taro, da sayar da kayyayaki ta hanyar watsa bidiyo kai tsaye, da dai sauransu. Ta wayar salula, kusan za a iya tafiyar da dukkan al’amuran yau da kullum a kasar. To, wannan irin saukin rayuwa, da saurin ci gaba da fasahohin zamani suke haifarwa tattalin arziki, da zaman al’umma, su ne abubuwan da kasar Sin ke son morewa tare da jama’ar kasashen Afirka, ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AfirkaCi GabaFasahaHadin GuiwaKimiyyaSin
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ana Gudanar Da Babban Taron Fasahohin Nuna Bayanai Na Kasa Da Kasa Na 2024

Next Post

An Kama Wani Matashi Mai Shekaru 25 Bisa Zargin Kashe Abokinsa A Kano

Related

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya
Daga Birnin Sin

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

1 hour ago
Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

3 hours ago
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
Daga Birnin Sin

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

3 hours ago
Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe
Daga Birnin Sin

Jami’i: Kasuwar Kasar Sin Ta Kasance Mai Jan Hankalin Zuba Jarin Waje A Ko Yaushe

20 hours ago
Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba Wajen Inganta Amfani Da Ruwa A Shekarar 2024

20 hours ago
Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata
Daga Birnin Sin

Alkaluman Adana Kaya Na Sin Sun Fadada Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata

22 hours ago
Next Post
An Kama Wani Matashi Mai Shekaru 25 Bisa Zargin Kashe Abokinsa A Kano

An Kama Wani Matashi Mai Shekaru 25 Bisa Zargin Kashe Abokinsa A Kano

LABARAI MASU NASABA

Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki

Hukumar NPA Ta Bayar Da Kwangilar Aikin Ruwa Na Tashar Lekki

June 7, 2025
Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya

June 7, 2025
Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

Gwamnatin Tarayya Da Hadin Gwiwar IFAD Za Su Yi Wa Manoma Rijista Domin Tantance Su

June 7, 2025
Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

Dalibai Sama Da Miliyan 13 Ne Za Su Rubuta Jarrabawar Shiga Jami’a Ta Kasar Sin

June 7, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka

June 7, 2025
Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

Sojojin Sama Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴan Ta’adda, Ya Daƙile Hari Ranar Idi A Borno

June 7, 2025
Afirka

2027: An Yi Kira Ga Masu Mulki Da Su Rungumi Tafarkin Inganta Rayuwar Al’umma

June 7, 2025
Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

June 7, 2025
Tufka Da Warwarar INEC Kan Yiwuwar Zaben 2023

Ana Ci Gaba Da Samun Rudani Yayin Da INEC Ta Jinkirta Rajistar Sabbin Jam’iyyu

June 7, 2025
Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

Manchester City Ta Kammala Daukar Tijjani Reijnders Daga AC Milan

June 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.