Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 25 mai suna Abba Garba Ibrahim da laifin kashe abokinsa mai suna Zaharaddeen Iliyasu mai shekaru 22 har lahira.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 29 ga Maris, 2024, a Chiranci Dorayi kwatas a Kano.
- Karin kudin Aikin Hajji: Gwamnatin Kebbi Za Ta Tallafawa Kowanne Maniyyaci Da Naira Miliyan 1
- Kano Ta Tallafawa Alhazai 2,096 Da Naira Biliyan 1.4
Kamar yadda wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan (PPRO) jihar ya fitar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce, an kira jami’ansu cewa, rikici ya barke tsakanin wasu abokanai biyu, hakan ya jawo daya ya buga wa daya wuka.
“Da isar jami’anmu, tuni an garzaya da gawar zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa nan take.”
An dai cafke wanda ake zargin ne, Abba Garba Ibrahim a hanyarsa ta tserewa zuwa Jamhuriyar Nijar.
“An mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yansanda, sashen kisan kai domin gudanar da cikakken bincike,” inji shi.
Talla