Telegram yana daya daga cikin manhajoji dangin su WhatsApp Snapchat da sauransu. Wata manhaja ce ta sada zumunta wadda ta fara aiki a shekarar 2013 wanda wasu yan kasar Rasha (Russia) suka kirkire ta, Nikolai da Pabel Durou kuma sune suka mallaki babbar kafar sadarwa ta kasar Rasha mai suna BK.
Kafar sadarwa ta Telegram kamfani ne mai zaman kansa da yake da mazauni na musamman a kasar Jamus (Germany) cikin wani gari mai suna Berlin, kuma Manhajar tana da rajista da LLP na ingilishi (English) da LLC na Amurka (America).
Da farko yaya za ka sauke manhajar Telegram a wayarka?
Idan kana so ka sauke shi a wayarka, to za ka shiga play store ne na cikin wayarka, sai ka yi searching din Telegram din. To za ka ganshi ya fito, sai ka yi download dinsa, wato ka sauke shi a kan wayarka. Shi ana yin rijista ne da lambar waya. Idan ka yi rijista zai nuna maka duk wadanda suke amfani da Telegram din daga cikin lambobin da ajiye a wayarka.
Telegram manhaja ce saukakakkiya da ake amfani da ita wajen saukake mu’amala da ‘yan’uwa da abokan arziki, tana saukaka huldar kasuwanci da mutanen da ke nesa ko na ketaren kasa da kasa, ana kuma iya tura sakonnin rubutu, hoto mai motsi da maras motsi (bideos da Pictures), sitika da kuma fayil (file) ko wane iri ne, ko da a ce girmansa da nauyin sa ya kai 1.5 GB ne, akwai damar zabin yin end-to-end encrypted.
Telegram ta ya yi kama da Manhajar WhatsApp kuma mafi kusa da manhajar tarho da tura sako ko kiran waya. Mai amfani da ita zai iya daura mata lambobi daban-daban har guda biyu a lokaci guda kuma ya karbi sako a kowannen su ta hanyar sanar dakai ta lambar da aka turo sakon ‘notification’ kuma zaka iya cire lambobin gaba daya daga kan manhajar, ma’ana kayi logging out din duka account biyu din a lokaci guda.
Har ila yau zaka iya canza lambar da ka bude Telegram din a duk sanda ka so kuma ba tare da ya bata wani lokaci ba, kari kan haka shi ne, mai amfani da manhajar zai iya mu’amala da mutane ba tare da sun ga lambar wayar sa ba, akasin WhatsApp da dole sai kana da lamba.
Manhajar Telegram tana iya daina amfani da kanta, ma’ana yakan iya goguwa bayan shafe watanni shida da ba tare da an yi amfani da shi ba. Amma manhajar ta saukaka ta yadda za a iya kara wa’adinsa har zuwa tsawon shekara guda kafin ya goge din.
Mutum yana iya boye lokacin hawansa ga kowa, ta yadda ko kana online ba za a san kana kai ba.
Da Me Manhajar Telegram Tafi Whatsapp?
Idan muka duba ko wanne daga cikin su da irin rawar da yake takawa wajen sada zumunta da kuma irin amfaninsa a soshiyal midiya. Za mu ga cewa ko wanne manhaja a cikin su tana kokarin kawo sauye sauyen da ya yi dai-dai da zamani da kuma bukatar masu ta’ammuli dashi wajen kawata Manhajar don burge masu amfani dasu.
Manhajar Telegram da WhatsApp suna da bambamce bambamce ta hanyar amfani da yawa, wanda a wani wajen sun hadu wani wajen kuma sun rabu. Mu dauki misalin Telegram a farko da wasu abubuwa da ya kunsa don saukake amfani da kuma kawata manhajar.
Ma’ajiyar gajimare (Cloud storage) wanda zai baka damar adana rubutu, hoto ko wani fayil mai muhimmanci, kuma hakan yana nufin ko da ka sauke lambar waya ka daura wata lambar daban to duk lokacin da ka bukaci dawo da lambar ka ta farko zaka dawo da ita cikin sauki ba tare da shan wata wahala ba sannan komai da komai da ka bari da suka hada da hoto ko bideo zaka tarar suna nan ba za su goge ba, hatta chatting din da ka yi da wani yana nan ba tare da tunanin yin backup ko restore ba.
Za ka iya sauke abu a duk lokacin da ka ke bukata kuma koda a ce abin da ka sauke din ya bace daga wayar ka, zaka iya komawa cikin manhajar ka sake sauke shi, ba kamar WhatsApp ba da sai dai a sake turo maka wani. Sannan idan kana bukatar tura ma wani abin da ka sauke ta kan manhajar Telegram (sharing) za ka iya tura masa cikin sauki ba tare da ka bata ‘data’ ko kwara daya ba, ta hanyar yin sharing zuwa akwatin karbar sakonsa (inbod).
Hoto inganci (kuality picture) Manhajar Telegram tana ba wa mutum zabin rage nauyin hoto ko bidiyo kafin turawa a cikin group ko pribate, ta yadda ba za a yi asarar ‘data’ mai yawa ba, idan kana so kana iya barinsa haka, amma rage nauyin ba yana nufin ingancin (kuality) hoton zai ragu ba ne.
Adadin mutanen da group yake iya dauka (group capacity) zaure a Telegram ya kan dauki adadi na membobi akalla 200, yayin da adadin ya cika kuma sukan karawa zauren guraben mutane 30,000 a wannan matakin zaure ya kan canza inganci daga yadda yake zuwa mafi inganci.
Sai kuma sunan amfani (User name) mutum ya kan iya mu’amala da wani ta Manhajar ba tare da yana da lambar wayar sa ba amma ta hanyar user name za a iya.
Za kuma ka iya bude channel a kan ita manhajar wanda zai baka damar tallata kasuwancin ka ko wani abu da ya yi kama da haka, saboda wani zaure ne da yake tara mutane masu yawan gaske, kowa yana iya shiga ba tare da ya cika ba kuma a kan tallata abubuwa da dama a cikinsa, musamman tashoshin Talabijin suna amfani da kafar Telegram wajen tallata shirye shiryensu. Sannan kana da ikon hana kowa magana a cikin group channel ta hanyar kulle akwatin rubuta sako na channel din ta yadda sai wadanda aka basu alhakin kula da zauren ne kawai suke da damar magana, sauran membobi kuma nasu karatu ne kawai.
Kana iya bude Channel kai kadai ta yadda zaka rinka ajiyar wasu muhimman rubututtukanka ko hoto ko bidiyo ko wani link.
Sannan manhajar Telegram tana amfani a wayoyi irin su, wayar Android, iOS, windows phone, windows pc, Mac OSD, Linud da sauran sashen bincike na browser da sauran abubuwa da suka bambanta ita manhajar da WhatsApp irin su secret chat, bots, support force, IFTTT integration, instant biew, draft, editing, wanda Idan Allah ya kai mu wani lokaci za muyi bayani a kan su.