Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta kulla da kamfanin Max Air da Air Peace domin jigilar alhazan shekarar 2024 zuwa kasar Saudiyya.
Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Arabi, wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyoyin da aka kulla a ‘Hajji House’ da ke Abuja a daren ranar Alhamis, ya bukaci kamfanonin jiragen samam da su nuna bajintarsu ta hanyar samar da abubuwa masu inganci ga alhazan Nijeriya.
- 2024 Hajj: Karancin Maniyyata Ba Nijeriya Kadai Ya Shafa Ba – NAHCON
- Da Dumi-dumi: NAHCON Ta Kara Wa’adin Biyan Kujerar Aikin Hajjin 2024
Arabi, ya kuma jaddada bukatar kamfanonin jiragen da su dauki tsaro da kare lafiyar mahajjata da muhimmanci.
Ya ce, ana tsammanin abubuwa masu yawa daga masu jigilar, yana mai tunatar da cewa, kar su manta, sai da aka tsaurara tantancewa kafin su tsallake bukatun acikin jerin kamfanonin da suka nemi a basu jigilar mahajjatan.