• English
  • Business News
Tuesday, August 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wadanda Suka Wawashe Hatsi A Kebbi Sun Shiga Firgici Bayan Kwace Buhun Shinkafa 2,000

by Sulaiman
1 year ago
in Labarai
0
kebbi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ranar Asabar da ta gabata, tun da sanyin safe matasa da mata da tsoffafi har da matan aure suka far ma sauran buhunan shinkafar Dangote da aka kai tallafi Jihar Kebbi inda suka wawashe akalla buhu dubu biyu.

Bayan samun wannan labarin abin da matasa da sauran jama’a suka aikata jami’an tsaro sun kawo dauki na gaggawa don ganin jama’a ba su wawashe shinkafar ba. Jami’an tsaro sun yi iya kokarisu wajen mai do da shinkafar da aka wawashe.

  • Karin kudin Aikin Hajji: Gwamnatin Kebbi Za Ta Tallafawa Kowanne Maniyyaci Da Naira Miliyan 1
  • Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Murabus Din Babban Limamin Masallacin Wala

Bayan aukuwar wannan ne, duk dai a ranar da misalin karfe daya na dare jama’a suka sake fitowa suka fasa rumbun ajiyar abincin da karamar hukumar Birnin Kebbi ta ajiye da zimmar rabawa ga jama’arta washe garin ranar Lahadi. A nan ma jami’an tsaron ‘yansanda da na Sojoji sun yi iya kokarinsu na ganin cewa jama’a basu wawashe dukkan abincin ba ta hanyar sanya barkonon tsohuwa amma duk da hakan bai hana aka wawashe wani sashe daga cikin abincin ba.

Yanzu hakan, a Jihar ta kebbi akwai labarin cewa jami’an tsaro sun samu nasarar cafke wasu daga cikin jama’ar da ake zargi da wawashe rumbun da kuma na wata mota a kusa dakasuwar kara da ke cikin garin Birnin Kebbi.

Ganin yadda abin ya auku bi da bi, sai ‘yansanda suka fantsama farautar mutanen da ake zargi da wawashe abincin. Bisa ga hakan hankalin jama’a a garin na Birnin Kebbi ya tashi, inda jama’a da dama suka shiga tsoro da farga.

Labarai Masu Nasaba

BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato

Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

Bugu da kari, bayan wuni daya an samu zaman lafiya a sassan Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi, sai kuma a washegari, dubban mutane ne suka tattara kansu tare da kutsawa cikin shagunan ‘yan kasuwa masu sayar da shinkafa da sauran hatsi iri-iri a unguwar Bayan-Kara, suka kwashe daruruwan buhuna.

Wani matashi, Abu Wanzan ya bayyana wa wakilinmu cewa, “yunwa da fatara ne suka sa jama’a suka kai hari kan wajen da ake ajiye abinci, haka kuma ba mu ji dadin yadda aka fara raba kayan abinci na baya-bayan nan da gwamnati ta sayo wa al’ummar jihar ba. Da yawa mazauna yankin garin Birnin Kebbi har yanzu ba su amfana da abincin da Gwamna Nasir Idris ya ce za a raba ma jama’a ba.”

Bisa abin da ya faru, ofishin mataimakin gwamnan jihar ya fitar da sanarwa, ta nuna rashin jin dadi game da lamarin tare da bayar da tabbacin cewa an dauki tsauraran matakan tsaro domin dakile sake afkuwar lamarin.

Hakazalika kwamishinan yada labarai da al’adu Alhaji Yakubu Ahmad Birnin Kebbi, ya sanar wa manema labaru da kafa kwamitin mutane 13 a karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar gona domin gudanar da bincike kan lamarin, wanda gwamnati ta bayyana a matsayin abin takaici da zargi.

Shi ma da yake jawabi ga manema labarai kwamishinan Ma’aikatar aikin goma da albarkatun kasa Alhaji Shehu Mu’azu ya bayyana cewa yawancin shinkafar da aka kwashe daga dakin ajiyar kaya dake Bayan-Kara mallakin karamar hukumar Birnin Kebbi ne a wani bangare na tallafin da gwamnatin jihar ta raba wa Kananan hukumomin 21na jhar.

Ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kwato buhunan abincin sama da 2,000 daga hannun jama’a tare da mayar da su inda aka ajiye su.

Alhaji Shehu Mu’azu wanda shi ne shugaban kwamitin binciken ya shaida wa manema labarai cewa an ba ‘yan kwamitinsa wa’adin kwanaki biyar daga ranar Litinin zuwa Juma’a domin su binciki musabbabin faruwar lamarin, da gano mutane ko kungiyoyin da ke da hannu tare da ba gwamnati shawara yadda ya kamata don kiyaye afkuwar lamarin.

A ranar Alhamis 21 ga watann Maris, ne Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya kaddamar da rabon tallafin abinci da suka hada da shinkafa, Dawa da sauran hatsi domin tausaya wa jama’ar jihar a watan Azumin Ramadan.

Bayan makonni kadan da ya kaddamar da rabon tallafin abincin ne kuma sai Gidauniyar Dangote ta bayyana nata rabon tallafin wanda daga bisani aka daka wawa a ragowar da ba a kai ga rabarwa ba ga al’ummar jihar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Jerin Manyan Attajiran Nijeriya A 2024

Next Post

Gwamna Uba Ya Umarci Kamo ‘Yan Kwangilar Da Suka Fara Aiki Suka Gudu

Related

BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato
Labarai

BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato

7 hours ago
Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

11 hours ago
Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe
Ra'ayi Riga

Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

11 hours ago
Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano
Manyan Labarai

Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano

12 hours ago
Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
Labarai

Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara

13 hours ago
Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa
Labarai

Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa

14 hours ago
Next Post
Kaduna

Gwamna Uba Ya Umarci Kamo 'Yan Kwangilar Da Suka Fara Aiki Suka Gudu

LABARAI MASU NASABA

BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato

BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato

August 4, 2025
Kasar Sin Ta Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Masu Samar Da Hidimar Intanet

Kasar Sin Ta Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Masu Samar Da Hidimar Intanet

August 4, 2025
Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Wasan Ƙwallon Kwando Ta Mata Da Dala $100,000 Kowace

Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Wasan Ƙwallon Kwando Ta Mata Da Dala $100,000 Kowace

August 4, 2025
Rundunar PLA Ta Yi Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin Cikin Shirin Ko Ta-Kwana

Rundunar PLA Ta Yi Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin Cikin Shirin Ko Ta-Kwana

August 4, 2025
Cinikin Kamfanoni a Kasar Sin Ya Ci Gaba Da Habaka Cikin Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Bana 

Cinikin Kamfanoni a Kasar Sin Ya Ci Gaba Da Habaka Cikin Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Bana 

August 4, 2025
Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15

Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15

August 4, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

August 4, 2025
Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

August 4, 2025
Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano

Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano

August 4, 2025
Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara

Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara

August 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.