Shugaban kasar Botswana ya yi barazanar tura giwa 20,000 zuwa Jamus a wata takaddama a tsakaninta da kasar.
A farkon wannan shekarar ne, ma’aikatar muhalli ta Jamus ta ba da shawarar cewa ka-mata ya yi a tsaurara matakai wajen shigar da lambobin karramawa da aka yi su sassan jikin dabbobin dajin da aka yi farautarsu.
- Akwai Tashoshin 5G Fiye Da Miliyan 3.5 A Kasar Sin
- Akwai Tashoshin 5G Fiye Da Miliyan 3.5 A Kasar Sin
Shugaban Botswana Mokgweetsi Masisi ya shaida wa wata kafar yada labaran Jamus cewa matakin zai jefa mutanen kasarsa cikin talauci ne kawai.
Ya ce adadin giwaye ya yi yawa ne saboda kokarin alkinta muhalli, farautar kuma tana taimakawa wajen rage adadinsu.
Ya kamata Jamusawa su “zauna tare da dabbobin, kamar yadda kuke kokarin fada ma-na,” in ji shugaba Masisi ga jaridar Jamus Bild. “Wannan ba abin wasa ba ne.”
Botswana, gida ce ga kusan kashi daya cikin uku na daukacin giwayen duniya – sama da 130,000 – fiye da yadda take da sararin kiwonsu.
Giwayen na yin barna ga dukiyoyi, suna cin amfanin gona tare da tattake mutanen karkara a yankunan, in ji shugaban.
A baya dai, Botswana ta bai wa makwabciyarta Angola giwa 8,000, sannan ta bai wa Mozambikue wasu daruruwan giwaye, a matsayin hanyar rage yawansu a kasar.
“Za mu so mu bayar da irin wannan kyauta ga Jamus,” in ji Masisi, ya kara da cewa ba zai yarda da a’a a matsayin amsa ba.
Ministan namun daji na Botswana Dumezweni Mthhimkhulu a watan da ya gabata ya yi barazanar tura giwaye 10,000 zuwa filin shakatawa na Hyde da ke Landan.
Kungiyoyin kare hakkin dabbobi suna jayayya cewa farautar dabbobi da harbin su san-nan a sarrafa sassan jikinsu kamar kai ko fatarsu, a matsayin lambar karramawa, zalunci ne kuma ya kamata a hana.
Jamus ita ce kasar Tarayyar Turai ta fi shigar da lambobin karramawa da aka yi su da sassan jikin giwa a nahiyar Afirka, a cewar wani rahoto na shekara ta 2021 na kungiyar Humane Society International.
Botswana ta haramta yin hakan a shekarar 2014, amma ta dage haramcin a 2019, bayan fuskantar matsin lamba daga al’ummomin yankin.
A yanzu dai kasar na fitar da kason farautar dabbobi a duk shekara, inda ta ce tana sa-mar da kyakkyawar hanyar samun kudin shiga ga al’ummar yankin, don haka ba su da sha’awar farautar namun daji, kuma tana da lasisi da kuma kula da su sosai.
A baya, an rika amfani da giwaye don yin abincin dabbobi.
Wata mai magana da yawun ma’aikatar muhalli a birnin Berlin ta shaida wa kanfanin dilancin labaren AFP cewa Botswana ba ta nuna damuwa da Jamus kan wannan batu ba.
Ta kara da cewa, “Saboda mummunan asarar da ake samu na bambancin halittu, muna da wani nauyi na musamman na yin komai don tabbatar da cewa shigo da lambobin karramawa da aka yi su sassan jikin giwa na farauta ya dore kuma ya zama doka,” in ji ta.
Ma’aikatar, ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Afirka da dokokin shigo da kayayyaki suka shafa, ciki har da Botswana, in ji kakakin.
Ostireliya da Faransa da kuma Belgium na daga cikin kasashen da suka haramta cini-kin lambobin karramawa da aka yi su da sassan jikin giwa da aka yi farauta
A watan Maris, ‘yan majalisar dokokin Burtaniya sun kada kuri’ar amincewa da dokar hana shigo da irin lambobin karramawar nan , amma dokar ta kara yin nazari kafin ta zama doka.
An sanya alkawarin hana shigo da lambobin karramawa da aka yi su da sassan jikin giwa a cikin kundin tsarin zabe na shekarar 2019 na jam’iyyar Conservative.
Ita ma Botswana da makwabciyarta Zimbabwe da Namibiya, sun yi zargin cewa kamata ya yi a bar su su sayar da tarin giwayen da suke da ita, ta yadda za ta samu kudi daga dimbin giwayenta.