Sa’o’i kadan bayan tsige Kwamared Philip Shaibu a matsayin mataimakin gwamnan jihar Edo, majalisar dokokin jihar ta rantsar da Omobayo Godwins mai shekaru 38 a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.
LEADERSHIP ta rawaito yadda aka tsige Shaibu a ranar Litinin, biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin bincike na mutum bakwai da majalisar ta kafa domin bincikar zarge-zargen da ake yi wa tsohon mataimakin gwamnan.
- ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Laftanar Din Soja A Yobe
- Majalisar Dokokin Edo Ta Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar
An rantsar da Omobayo Godwins da misalin karfe 1:30 na rana a gidan gwamnati da ke Jihar.
Wane ne Injiniya Omobayo Godwins?
An haife Marvelous Omobayo Godwins a ranar 19 ga watan Yuli, 1986, a karamar hukumar Akoko Edo ta Jihar Edo.
Ya mallaki digiri a bangaren Injiniyan Wutar Lantarki da digiri na biyu a Jami’ar Benin (UNIBEN).
Bayan nasarorin da ya samu daban-daban, Omobayo ya shiga harkokin siyasa a karamar hukumarsa, inda ya yi gwagwarmaya.
Da yake jawabi bayan nadinsa, Injiniya Omobayo ya bayyana kudurinsa na yin amfani da iliminsa domin ciyar da Jihar Edo gaba.