Rundunar ‘yansandan jihar Neja, ta haramta hawan dawaki a babban birnin jihar, Minna yayin bukukuwan karamar Sallah.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Shawulu Ebenezer danmamman ne, ya bayyana wannan mataki a sakon sallar da ya aike wa jama’a cikin wata sanarwa.
- HOTUNA: Yadda Aka Yi Jana’izar Jaruma Sataru Daso
- Za A Gurfanar Da Ganduje A Kotu Kan Zargin Cin Hanci Da Rashawa A Kano
Neja ta yi kaurin suna wajen samu hare-haren ‘yan daba a lokacin bukukuwan sallah wadanda ke fakewa da hawan dawakin da jama’a ke yi.
A cewar sanarwar yanzu haka an rarraba jami’ai 2,500 a sassan jihar don bayar da kariya a filayen sallar idi da ke kananan hukumomin jihar 25 baya ga wuraren shakatawa da sauran wajen taruwar jama’a.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da damar bikin sallar wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassan jihar dama sauran jihohin Nijeriya.