Rundunar sojin saman Nijeriya (NAF), ta tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda – Abdullahi Nasanda da Mallam Tukur a wani hari ta sama da ta kai a kananan hukumomin Zurmi da Maradun a jihar Zamfara.
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Vice Marshal Edward Gabkwet a cikin wata sanarwa, ya ce, hare-haren da rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta kai a ranar 10 ga Afrilu, 2024 ya kai ga kawar da ‘yan ta’adda da dama tare da tarwatsa sansanoninsu.
- Yadda Jami’in Tsaro Ya Bindige Wani Mutum Ana Tsaka Da Sallar Idi A Zamfara
- Jihar Zamfara Ta Haramta Zirga-zirga A Tsakanin Iyakokinta Da Katsina Da Sokoto Daga Karfe 7 Na Yamma
Ya ce, aikin leken asiri, sa ido da kuma bincike (lSR) da aka gudanar a sansanin Abdullahi Nasanda ne ya bankado maboyar ‘yan ta’aaddn da ke boye cikin bishiyoyi.
ISR ta kuma gano wasu babura nasu da aka boye karkashin bishiyoyi.
Ya kara da cewa, an kuma kai makamancin wannan hari ta sama a wani sansanin ‘yan bindiga da ke cikin garin Maradun, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara